Babu wata rigima tsakani na da Adams Oshiomhole – Inji Gwamna Obaseki

Babu wata rigima tsakani na da Adams Oshiomhole – Inji Gwamna Obaseki

Gwamnan jihar Edo, mai girma Godwin Obaseki ya yi watsi da rade-radin da a ke yi na cewa ya na fada da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, kamar yadda wasu ke yadawa.

Godwin Obaseki ya nuna cewa sam babu wata rigima da ta shiga tsakaninsa da tsohon gwamnansa Adams Oshiomhole. Gwamnan ya bayyana wannan ne wajen wani taro da a ka yi jiya a Abuja.

An shirya wannan taro da kungiyar Usagbe ta saba yi duk shekara ne wannan karo a 7 ga Watan Yunin 2019. Gwamnan ya yi amfani da wannan dama wajen rabe zare da abawar rade-radin da ke yawo.

“Babu wani rikici tsakanin na da shugaban jam’iyya. Wasu sababin siyasa ne su ka bijiro a jihar Edo, kuma mun warware matsalolin.” Gwamna Godwin Obaseki ya yi wa jama’a karin haske.

Gwamnan ya kara da cewa:

KU KARANTA: Adams Oshiomhole ya bayyana a gaban kotun karar zaben 2019

“Ainihin abin da ya faru shi ne sabanin majalisa, kuma wannan ba wata babbar matsala ba ce. Wasu ‘yan majalisa ne su ka ki bari a kadammar da su, kuma nan gaba na san za a kaddamar da su din.”

Obaseki ya nuna cewa yanzu batun na gaban kotu, kuma Alkalai masana za su yanke hukunci. Gwamnan ya ce shi ba kwararre ba ne a kan sha’anin dokar kasa da har zai yi magana kan batun.

“Idan kun san abin da ya faru a 2006, an samu wasu baren gwamnati da su ka samu daurin gindin manyan ‘yan siyasa, su na yin yadda su ka ga dama; su na karbar haraji. Sun zama gwamnatin kan-su.”

Mai girma gwamnan ya nuna cewa dole ya takawa irin wadannan mutane burki a Edo domin kawowa jihar kudin-shiga, tare da kuma kafa doka da tsari. Gwamnan ya ce wannan ba bakon abu ba ne.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel