Rundunar soji ta ceto manoma 13 daga hannun masu garkuwa da mutane a Kaduna (hotuna)

Rundunar soji ta ceto manoma 13 daga hannun masu garkuwa da mutane a Kaduna (hotuna)

- Rundunar soji ta ceto manoma 13 da aka yi garkuwa das u a jihar Kaduna

- A cikin haka, an kashe daya daga cikin masu garkuwa da mutanen yayinda sauran suka tsere da harbin bindiga

- Ana ci gaba da kokarin ganin an kama sauran yan bindigan da suka tsere

Rundunar soji a ranar Litinin, 8 ga watan Yuli, ta ceto manoma 13 da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

A cikin hakan, an kashe dan ta’adda daya yayinda suke arangama da dakarun sojin.

Kanal Sagir Musa, daraktan harkokin jama’a na rundunar ne ya bayyana hakan a shafin Facebook.

“Wata tawagar sintiri na rundunar sojin Najeriya daga sansanin Kuyello a karamar hukumar Birnn Gwari da ke jihar Kaduna sun ceto wasu manoma 13 da yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin. An kashe dan ta’adda daya a yayinda suke arangama da sojoji,” ya rubuta.

KU KARANTA KUMA: Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya ziyarci Tinubu

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa ana cigaba da garkuwa da mutane da a hanyar Abuja zuwa Kaduna yayinda yan bindigan sukayi awon gaba da fasinjojin mota kirar Golf da safiyar Litinin, 8 ga watan Yuli, 2019.

Yan bindigan sun tare da babbar titin Abuja zuwa Kadunan ne a daidadi gonar Mikati da jami'an yan banga ke tsayawa.

Wani mai idon shaida mai suna Idris Sa'idu ya bayyana hakan ne a shafin ra'ayi da sada zumuntarsa na Facebook cewa saura kiris abin ya rutsa da su amma Allah ya kiyaye.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel