Yanzu-yanzu: An gurfanar da Sanata Elisha Abbo a kotu

Yanzu-yanzu: An gurfanar da Sanata Elisha Abbo a kotu

- An garzaya da Sanata Elisha Ishaku Abbo kotun shari'a

- Abbo zai gurfana ne kan laifin cin zarafin dan Adam

- Sanata ya amsa wannan laifi kuma ya bukaci al'ummar Najeriya su yafe masa

Hukumar yan sandan Najeriya hallaro da Sanata Elisha Abbo kotun Majistare dake unguwar Zuba, Abuja domin gurfanar da shi kan laifin cin zarafi.

Jaridar Punch ta bada rahoto ranar Lahadi cewa hukumar yan sanda za ta gurfanar da Sanatan a wannan mako bayan abubuwan da suka faru a makon da ya gabata.

Hakazalika kwamishanan yan sandan birnin tarayya, Bala Ciroma, ya tabbatar da labarin cewa an kai Sanata Elisha Abbo kotu.

Yace: " (Yan sanda) Sun kaishi kotun majistare dake Zuba domin gurfanar da shi. Suna kan hanyarsu yanzu."

An tattaro cewa masu gudanar da bincike sun tabbatar da cewa lallai hujjan da aka gabatar kan sanatan jam'iyyar PDP, Elisha Abbo, mai wakiltar Adamawa ta Arewa inda yake ya waskawa wata matar aure mari gaskiya ne.

KU KARANTA: Akalla mutane 19 sun hallaka, 7 sun jikkata yayinda motoci 4 sukaci kicibis a jihar Kano

Hakazalika Sanata Abbo ya amsa wannan laifin a jawabin da ya gabatar a hedkwatan jam'iyyar PDP a makon da ya gabata inda ya nemi gafarar matar, matan Najeriya, da kuma yan kasa ga baki daya.

Wannan kadai ya isa ya zama hujja akansa a gaban kotu.

A ranar Laraba hukumar ta gayyaci sanatan kuma ya amsa gayyatar ranar Alhamis inda ya sha tambayoyi har sai da ya kwana a ofishin yan sanda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel