Tirkashi: An samu rabuwar kai a tsakanin gwamnonin PDP

Tirkashi: An samu rabuwar kai a tsakanin gwamnonin PDP

- Rikicin PDP a majalisar wakilai na barazanar tarwatsa jam’iyyar adawa

- Ga dukkan alamu kawunan gwamnonin PDP ma ya rabu yayinda suke goyon bayan bangarori daban daban a majalisar

- Babu alamun cewa rikicin jam'iyyar zai kare a halin yanzu

Rahotanni sun bayyana dalilin da yasa wasu gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), suka yi shuru akan rikicin da ya kunno kai a jam’iyyar dangane da dakatar da Hon. Ndudi Elumelu da sauran mambobi shida na jam’iyyar a majalisar wakilai.

Kwamitin PDP a makon da ya gabata ta dakatar da Elumelu, Wole Oke, Lynda Ikpeazu, Anayo Edwin, Gideon Gwani, Toby Okechukwu da Adekoya Abdul-Majid kan rikicin da ya shafi zaben shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai.

A cewar rahoton, wasu gwamnonin PDP basu ji dadin hukuncin da ya fito daga takwaransu na jihar Rivers, Nyesome Wike ba, wanda suka zarga da tsayar da Hon. Kingsley Chinda a matsayin shugaban marasa rinjaye a majalisar.

Chinda, 53 ya kasance dan jihar Rivers tare da Gwamna Wike da wani mamba wanda ya shafe karo uku a majalisar wakilai.

Wata majiya ta kusa da gwamnan PDP din tace wasu daga cikin gwamnonin sun ce tunda jihar Rivers ta tsayar da Shugaban jam’iyyar na kasa, ya kamata ace wata jiha a yankin Kudu ta tsayar da shugaban marasa rinjaye don adalci da gaskiya.

Majiyar ta kara da cewa wasu gwamnoni basu ji dadin yanda Wike ya dauki lamarin jam’iyyar ba idan aka tuna yanda gwamnan ya janyo matsala a jam’iyyar a lokacin da ya tsayar da Sanata Ali Modu Sheriff a matsayin Shugaban jam’iyyar na kasa.

Wani dan majalisa daga PDP wanda ya nemi a boye sunansa yayi tuni akan yanda Wike ya razana shugabancin jam’iyyar a harabar zaben fidda gwani na shugaban kasa na PDP a 2018 a lokacin da wasu masu ruwa da tsaki suka nuna rashin amincewarsu kan gudanar da zaben a Port Harcourt.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Karo na farko Oshiomhole ya bayyana a kotun zaben Shugaban kasa

Dan majalisan ya kara da cewa wasu masu ruwa da tsakin Jam’iyyar sun kasance cikin damuwa a lokacin da Wike ya zama mai fada aji a jam’iyyar, inda ya kara da cewa gwamnan na jihar Rivers ba kowa bane a 1998 a lokacin da aka kafa kungiyar G-32 a jam’iyyar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel