Yanzu Yanzu: Karo na farko Oshiomhole ya bayyana a kotun zaben Shugaban kasa

Yanzu Yanzu: Karo na farko Oshiomhole ya bayyana a kotun zaben Shugaban kasa

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, Adams Oshiomhole, a ranar Litinin, 8 ga watan Yuli yayi bayyanarsa ta farko a kotun sauraron kararrakin zaben Shugaban kasa a Abuja, tun bayan kaddamar da zaman wanda ya fara a ranar 10 ga watan Yuni.

Jam’iyyar Peoples Democratic Party da dan takararta a zaben Shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairu, Alhaji Atiku Abubakar, sun shigar da kara kotun inda suke kalubalantar sakamakon zaben wanda jam’iyyar APC da dan takararta, Shugaban kasa Muhammadu Buhari suka yi nasara.

Oshiomhole ya isa kotun da misalin karfe 9:36 na safiyar ranar Litinin yan mintuna kadan kafin fara zaman kwamitin mutum biyar karkashin jagorancin Justis Mohammed Garba.

Ya zauna a tsakakkanin tsohon Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa kuma jigon APC daga jihar Adamawa, Nuhu Ribadu da kuma wani jigon PDP, Tom Ikimi.

KU KARANTA KUMA: Sabbin masarautun da aka kafa za su ci gaba da kasance har abada - Ganduje

A daya gefen Ikimi kuma ya kasance kakakin jam’iyyar APC, Kola Ologbodiyan.

A lokacin da aka fara zaman, Oshiomhole ya bayyana kansa a matsayin wakilin Buhari da APC, yayinda Ologbodiyan ya wakili PDP.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP da dan takararta, Atiku Abubakar, sun gabatar da tsohon abokin Buhari, Buba Galadima, matsayin mai bada shaida.

Tun shekarar 2003 da shugaba Muhammadu Buhari ya fara takarar kujeran shugaban kasan Najeriya, Buba Galadima ya kasance babban na hannun damarsa har zuwa 2015 da ya samu nasarar danewa kujerar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel