Da duminsa daga kotun zaben shugaban kasa: An gabatar da Buba Galadima matsayin mai bada shaida

Da duminsa daga kotun zaben shugaban kasa: An gabatar da Buba Galadima matsayin mai bada shaida

Labari kai tsaye daga kotun daukaka kara inda ake shari'a kan zaben shugaban kasan 2019, jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP da dan takararta, Atiku Abubakar, sun gabatar da tsohon abokin Buhari, Buba Galadima, matsayin mai bada shaida.

Tun shekarar 2003 da shugaba Muhammadu Buhari ya fara takarar kujeran shugaban kasan Najeriya, Buba Galadima ya kasance babban na hannun damarsa har zuwa 2015 da ya samu nasarar danewa kujerar.

Amma gab da karewa wa'adin Buhar na farko, Buba Galadima ya fara nuna adawa da gwamnatin Buhari kuma ya hada kai da jam'iyyar PDP duk da cewa yana cigaba da ikirarin cewa shi dan jam'iyyar APC ne har yanzu.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An yi garkuwa da mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Mun kawo muku a baya cewa dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin lemar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), da jam'iyyarsa sun gabatar da hujjoji 26,175 kan zaben shugaba Muhammadu Buhari a kotun zaben shugaban kasa dake Abuja.

Lauyan Atiku, Livy Uzoukwu, ya fara gabatar da hujjoji 5,196 ranar Alhamis, kafin ya gabatar da sauran ranar Juma'a.

Atiku yana kulabalantar nasarar da shugaba Muhammadu Buhari ya samu inda yace kuri'un da ya samu ya fi na shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) yawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel