Sabbin masarautun da aka kafa a Kano za su ci gaba da kasancewa har abada - Ganduje

Sabbin masarautun da aka kafa a Kano za su ci gaba da kasancewa har abada - Ganduje

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayyana cewa masarautu hudun da aka kafa sun zaunu sannan kumaa cewa za su ci gaba da kasance har abada.

Har ila yau gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar zata inganata babbar asibitocin da ke cikin hedikwatar sabbin masarautu hudun da aka kafa zuwa karfinmai daukar gadaje 400, don inganta tsarin kiwon lafiya.

Ganduje yace manufar yin hakan ba komai bane illa kara inganci da sanayya, tare da karfafa dalilan kafa sabbin masarautu a jihar.

Ya bayyana hakan ne a ranan Lahadi a lokacin da ya kai gaisuwar ta’aziyya ga sarkin Rano, Alhaji (Dr) Tafida Abubakar (Autan Bawo), kan mutuwar dansa, Aliyu Tafida mai shekara 20 da haifuwa. Yayi addu’a kan Allah ya gafarta wa mamacin.

Ganduje ya jaddada cewa daga cikin manyan dalilan da yasa aka kafa sabbin masarautun ba komai bane illa saukaka rayuwa ga al’umman da ke zama a masarautun guda hudu. Tare da samar da cigaba a dukkan yankunan jihar.

Gwamna Ganduje yayi tuni cewa cibiyoyin al’adun gargajiya ne mai hada hannu tare da gwamnatin dake mulki don inganta jihar, wanda ke samar da damar rayar da cigaba ga mai dorewa a dukkan sashe ga al’umma.

Hadin gwiwa tsakanin gwamnati da cibiyoyin gargajiya, a cewar shi yana da muhimmanci ga cigaban al’umma a fannin tsaro, kiwon lafiya, ilimi, muhalli da zamantakewa da sauransu.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe mutane 8 a kauyukan Katsina

Akan batun sanar da karatun firamare da sakandare kyauta, Ganduje ya bayyana cewa saboda muhimmancin dake tare da shi, za a kafa kwamiti na musamman tare da hadin gwiwar cibiyoyin gargajiya don ganin an aiwatar da manufofi a fadin dukkan lungu da sako na jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel