Kashe-kashe: Kungiyoyi sun yi wa Soji raddi, sun nemi Buhari ya canza zani

Kashe-kashe: Kungiyoyi sun yi wa Soji raddi, sun nemi Buhari ya canza zani

Jam’iyyar PDP mai adawa da kuma kungiyoyi irin su Ohanaeze Ndigbo wanda a ka fi sani da SERAP da Ohanaeze Ndigbo sun nemi Shugaban kasa Buhari ya canza manyan Hafsun Sojin Najeriya.

Rahotanni sun zo mana cewa wadannan kungiyoyi masu zaman kan-su sun yi kira ga shugaban kasar da ya sake Hafsun sojojin sama da na kasa domin a cewarsu, ba a ganin tasirin aikin da su ke yi a yanzu.

Hakan na zuwa ne bayan da manyan sojojin su ka fito su ka furta cewa irin shirin da su ke yi, ya na aiki. Wadannan kungiyoyi na SERAP da Ndigbo sun ce irin kashe-kashen da a ka yi a kasar ya yi yawa.

Sakataren yada labarai na PDP, Kola Ologbondiyan, ya ce tun da Sojoji su ka fito su ka ce aikinsu na kyau, a ke kashe jama’a a kasar. Ologbondiyan ya ce kwanan nan a ka kai wasu hari a wata jihar Arewa.

Mai magana da bakin jam’iyyar PDP ya ke cewa:

KU KARANTA: Boko Haram sun kwashi kashinsu a hannun Sojojin Najeriya

“Ba mu gamsu da halin tsaron da a ke ciki a kasar nan ba. Kamar yadda mu ka saba fada, ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake yi wa kusoshin tsaron kasar gyaran hamma”

Takwaransa na kungiyar Kabilar Ibon kasar Ohanaeze Ndigbo mai suna Uche Achi-Okpaga, ya bayyana irin haka a wata hira da ya yi da Manema labarai inda ya ce ya kamata Buhari ya kawo canji.

“Har gobe a na aukawa gonaki da kauyuka, a na kashe jama’a. Ta ya za a ce sojoji na aiki a lokacin da gwamnati ke cire kudi domin sayen makamai, yayin da ‘yan ta’adda su ke kashe Dakarun Najeriya?” Inji Achi-Okpaga.

Shi ma shuganan kungiyar SERAP, Adetokunbo Mumuni, ya na tare da babbar jam’iyyar hamayyar Najeriya ta PDP ya na mai cewa ta tabbata akwai bukatar Buhari ya kawo sababbin jini a gidan soja.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel