Jam'iyyar PDP na gab da rushewa idan har aka tursasa Chinda a matsayin shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai – Matasan PDP

Jam'iyyar PDP na gab da rushewa idan har aka tursasa Chinda a matsayin shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai – Matasan PDP

Wata kungiyar matasan PDP mai suna Youths Movement of Peoples Democratic Party (PDP) tae tursasa Kyingsley Chinda a matsayin Shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai na iya rusa jam’iyyar adawar.

Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai, ya sanar da Ndidi Elumelu a matsayin sugaban marasa rinjaye amma jam’iyyar PDP ta ki amincewa da hakan.

Daga baya sai PDP ta dakatar da Elumelu da wasu yan majalisa guda shida. Elumelu ya bayyana dakatarwar da aka yi masa a matsayin gaggawa.

A wani jawabi a ranar Asabar, Tony Ayaegbunem, jagoran kungiyar, ya sha alwashin hana duk wani yunkuri na PDP wajen tursasa Chinda a matsayin Shugaban marasa rinjaye.

Ayaegbunem yace dakatarwar da aka yi wa yan majalisar baya bisa ka’ida duba ga kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe mutane 8 a kauyukan Katsina

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Kwamitin gudanar wa (NWC) na jam'iyyar PDP ya sanar da dakatar da Honarabul Ndudi Elumelu da sauran wasu mambobin ta shida a majalisar wakila.

Ragowar mambobin shida su ne; Honarabul Wole Oke, Honarabul Lynda Ikpeazu, Honarabul Anayo Edwin, Honarabul Gideon Gwadi, Honarabul Toby Okechukwu da Honarabul Adekoya Abdulmajid.

A ranar Alhamis ne NWC ya gayyace su domin amsa tuhumarsu da aikata laifukan haddasa rikicin shugabanci a tsakanin mambobin jam'iyyar a zauren majalisar wakilai ranar Laraba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel