Hankula sun tashi a Ibadan saboda hana dalibai mata sanya Hijabi a makarantar sakandari

Hankula sun tashi a Ibadan saboda hana dalibai mata sanya Hijabi a makarantar sakandari

Kungiyoyin Musulunci sun bara tare da nuna bacin ransu game da yadda hukumar makarantar sakandarin jami’ar Ibadan ta jahar Oyo take tilasta ma dalibai mata Musulmai su cire hijabansu, duk da cewa dokar makarantar bata hana ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito an sha kwaramniya tsakanin iyayen yara da shugaban makarantar sakandarin Phebean 0. Olowe akan batun sanya Hijabi, inda iyayen suka nemi hukumar makarantar ta kyale yaransu su sanya Hijabi kamar yadda dokar kasa ta basu dama.

KU KARANTA: NNPC: Mele Kyari ya canji Maikanti Baru a kamfanin mai na kasa

Kungiyoyin Musulunci kamarsu ISI, MPF da MURIC sun yi gargadin cewa wannan mataki da shugaban makarantar ta dauka ya fara wuce gona da iri, kuma a matsayinsu na Musulmai ba zasu lamunci cin mutuncin yayansu musulmai ba.

Shugaban ISI, Abdulrahman Balogun yace biyo bayan shawarar da suka yanke na janye karar da suka shihgar da hukumar makarantar a gaban babbar kotun jahar akan batun sanya Hijabi a ranar Yunin shekarar 2019, shugaban makarantar tare da ma’aikatanta suna cin zarafin daliban da suka dage akan sanya Hijabi, har maganar ta kai ga kotu.

Shima shugaban MURIC, Ishaq Akintola ya koka kan bidiyon daya kalla na yadda hukumar makarantar ke tilast ma dalibai cire Hijabi, inda yace abin kunya ne ga jami’ar Ibadan a matsayinta na dadaddiyar jami’a a Najeriya.

Daga karshe kungiyoyin sun yi kira ga hukumomi da su shiga maganar kafin matakin da makarantar ta dauka na hana musulmai sanya Hijabi ya janyo tashin hankali, wanda ba’a san iyakan inda zai tsaya ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel