Sojoji sun tafka ma kungiyar Boko Haram mummunan ta’asa a Borno

Sojoji sun tafka ma kungiyar Boko Haram mummunan ta’asa a Borno

Dakarun rundunar Sojan sama sun kaddamar da mummunan hari akan mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram a garin Bakassi na jahar Borno, inda suka tafka musu babbar asara tare da halaka yan ta’adda da dama.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito kaakakin rundunar Sojan sama, Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 7 ga watan Yuli, inda yace rundunar ta kaddamar da harin ne a ranar 6 ga watan Yuli.

KU KARANTA: NNPC: Mele Kyari ya canji Maikanti Baru a kamfanin mai na kasa

A yayin wannan hari, Sojojin san yi amfani da manyan jiragen yaki wajen zazzaga ma mayakan Boko Haram bama bamai a yankin Bakassi tare da lalata wasu gine gine da kungiyar take amfani dasu.

A cewar kaakakin, bayan harin farko da rundunar ta kaddamar, sai kungiyar ta kwashe ragowar mayakanta da sauran kayan aikinta zuwa wani mafakarsu, samun wannan bayani yasa rundunar ta sake aika jiragen yaki kirar Alpha wanda suka sake tarwatsasu ta hanyar saukan musu da ruwan bama bamai.

“Mun samu bayanan safarar mayakan Boko Haram da kayan aikinsu zuwa wani sansani na daban, samun wannan labari keda wuya muka aika da jiragen Alpha Jet guda 2 wanda suka yi musu ruwan wuta tare da kashe yan ta’adda da dama, da kuma lalata sansanin nasu, har ma da ragowar kayan aikinsu.” Inji shi.

Daga karshe Daramola yace rundunar Sojan sama zata cigaba da kokarin kakkabe ragowar mayaka yan ta’adda da suka rage a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, dama Najeriya gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel