NNPC: Mele Kyari ya canji Maikanti Baru a kamfanin mai na kasa

NNPC: Mele Kyari ya canji Maikanti Baru a kamfanin mai na kasa

A jiya Lahadi 7 ga Watan Yuli, 2019, Dr. Maikanti Baru ya cika shekaru 60 a Duniya. Hakan na nufin dole ya yi ritaya, ya ajiye aiki. Wannan ya sa wani sabon shugaba zai karbi ragamar NNPC.

Maikanti Baru ya yi ritaya daga kamfanin mai na kasa na NNPC ne a Ranar Lahadi, inda Mele Kyari zai karbe sa. NNPC ta tabbatar da tafiyar Maikanti Baru tare da shirya masa walimar bankwana.

Dr. Baru da kan-sa ya bayyana wannan a shafin sa na Tuwita inda ya rubuta:

“A yau na cika shekaru 60 cir na aiki, na yi ritaya daga kamfanin NNPC na kasa. Ina yi wa sabon babban Manajan kamfanin, Malam Mele Kolo Kyari da Tawagarsa fatan alheri.”

Har wa yau Baru ya kara da cewa:

KU KARANTA: Wasu mutum 3 da Buhari zai ba Minista wannan karo

“Ina mika godiya ta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bani damar yi wa kasa aiki. Allah ya taimaki kamfanin NNPC. Allah ya taimaki kasar mu Najeriya!”

Kwanakin baya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mele Kolo Kyari a matsayin shugaban hukumar na 19 a tarihi wanda zai canji M. Baru a yau ganin shekarunsa sun cika.

NNPC ta bayyana cewa ta shirya liyafa domin yin bankwana da Maikanti Baru. Za a yi wannan biki ne a cikin ginin na NNPC da ke Abuja yau 8 ga Watan Yuli, 2019 inji Kakakin kamfanin man.

Kyari zai soma aiki ne a an jima a matsayin sabon GMD. Ganin cewa jiya Lahadi ba ranar aiki ba ce, shiyasa a ka shirya yin wannan bankwana yau inji Ndu Ughamadu mai magana da yawun NNPC.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel