Jigo a APC ya bayyana sunayen mutane 3 da ke cikin sunayen sabbin ministoci

Jigo a APC ya bayyana sunayen mutane 3 da ke cikin sunayen sabbin ministoci

Wani jigo a jam'iyyar APC ya bayyana cewa yanzu haka jam'iyyar na kokarin dinke barakar ta tare da hada kan 'ya'yanta ta hanyar sake sabon zubi a kunshin kwamitin gudanarwa (NWC) na jam'iyyar.

Ya ce tuni aka mika sunayen mambobin NWC na yanzu domin a basu mukaman ministoci, wasu kuma a nada su jakadun Najeriya a kasashen ketare.

Ya kara da cewa wannan karon jam'iyyar APC za ta saka wa 'ya'yanta da suka wahalta mata a baya.

"Za a bawa wasu daga cikin mambobin NWC na yanzu mukamin minista, yayinda wasu za a nada su jakadai a kasashen ketare.

"Daga cikin wadanda za bawa minista akwai shugaban jam'iyya na kasa, kwamred Adams Oshiomhole (jihar Edo); mataimakin shugaban jam'iyya na yankin kudu, Cif Niyi Adebayo (jihar Ekiti) da babban mai bincike na jam'yya, Cif George Moghalu (jihar Anambra)," a cewar majiyar.

Kwamitin NWC na APC na da mambobi 21, kuma ana sa ran a kalla 12 daga cikinsu za su samu mukamai a sabuwar gwamnatin Buhari ta biyu.

DUBA WANNAN: Rashin sani: Yadda dangin amarya suka kashe ango dan jihar Borno da abokansa 7 a jihar Adamawa

Amma da aka tuntubi mai bincike na kasa, Cif George Moghalu, ya ce bashi da masaniya a kan maganar.

Ya ce: "ni ma wannan shine karo na farko da na ke jin wanna magana. Ba ni da masaniyar akwai wani tsari irin wannan. Kun ce wata majiyar fadar shugaban kasa ce ta sanar da ku hakan, ba zan iya sanin gaskiyar maganar ba tunda ba zaku iya nuna min wanda ya fadi hakan ba a fadar shugaban kasa."

Sai dai wasu na ganin yin hakan ba zai haifar da zaman lafiya a cikin jam'iyyar APC ba.

A kwanakin baya ne mataimakin shugaban jam'iyyar APC na yankin arewa, Muhammed Lawal, ya yi kira ga Oshiomhole da ya yi murabus biyo bayan asarar wasu kujerun gwamnoni da APC ta yi a zaben da ya gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel