Son zuciya da son kai ya sanya matatun man fetur na Najeriya suka lalace - Shehu Sani

Son zuciya da son kai ya sanya matatun man fetur na Najeriya suka lalace - Shehu Sani

- Sanata Shehu Sani ya alakanta lalacewar matatun man fetur na kasar da son zuciya da kuma son kai

- Tsohon Sanatan ya ce masu hannu cikin tsiyar da lalata matatun su ke cin moriyar arzikin man fetur a kasar nan

Tsohon wakilin shiyyar Kaduna ta Tsakiya a zauren majalisar dattawan Najeriya, Sanata Shehu Sani, ya yi furuci a kan yadda matatun man fetur suka lalace a Najeriya tare da fayyace masu hannu cikin dashen wannan mummunar tsiya.

Sanatan cikin wani sako da ya wassafa a shafin sa na zauren sada zumunta a ranar Lahadi 7 ga watan Yulin 2019, ya ce wadanda suka dasa tsiyar da ta gurbata matatun man fetur sun kasance masu son gwamnatin ta yi masu bajakoli domin su saya cikin rahusa da manufar tara dukiya.

Tsohon Sanatan na jihar Kaduna bai takaita a nan ba kadai, ya kuma alakanta kalubalen da matatun man fetur suka yi tsamo-tsamo a ciki a sanadiyar son zuciya na masu shigo da man fetur kasar nan wajen cin moriya iyaka kawunan su da nuna halin ko in kula ga ci gaban kasa.

KARANTA KUMA: Gwamna Dickson ya yabawa Buhari kan nadin sakataren gwamnatin Tarayya

Kazalika tun a ranar Laraba 24, ga watan Afrilun da ya gabata, karamin ministan man fetur na kasa, Ibe Kachikwu, ya ce Najeriya ta na bukatar kimanin Naira biliyan 900 domin gyara na sake dawo da martabar matatun man fetur na kasar nan.

Furucin ministan ya zo ne a birnin Riyadh na kasar Saudiya yayin ganawar sa da ministan masana'antu na kuma ma'adanan kasa na kasar ta Saudiya, Khalid Al Falih.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel