Gwamna Dickson ya yabawa Buhari kan nadin sakataren gwamnatin Tarayya

Gwamna Dickson ya yabawa Buhari kan nadin sakataren gwamnatin Tarayya

Gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, ya kwarara yabo tare da jinjina a kan shugaban kasa Muhammadu Buhari dangane da sake zaben Boss Mustapha, a matsayin sakataren gwamnatin Tarayyar kasar nan.

Gwamnan cikin wani jawabi da sanadin mai magana da yawunsa, Fidelis Soriwei, ya hikaito furucin uban gidan sa a kan sake nada Boss Mustapha da ya misalta a matsayin kyakkyawan yunkuri na dace kuma macancanci.

Ya yi bayanin cewa, babu shakka sakataren gwamnatin Tarayyar kasar nan ya yi kwazon gaske wajen sauke nauyin da rataya a wuyan sa cikin karamci da kuma martaba.

Gwamna Dickson ya kuma jaddada yabo ga shugaban kasa Buhari da bisa ga cancanta ya sake maimaita zaben Boss Mustapha a matsayin sakataren gwamnatin Tarayya a wa'adi na biyu da hakan yake nuna yabawa kwazon da yayi wajen sauke nauyin da rataya a wuyansa.

A yayin taya murna da kuma son barka, gwamnan jihar Bayelsa ya yi fatan sakataren gwamnatin Tarayyar kasar nan zai ci gaba da bibiya da kuma cin gajiyar kyakkyawan tafarkin da ya assassa na yiwa shugaba Buhari hidima da sauke nauyin kasa da rataya a wuyan sa.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari da sanadin mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu, a ranar Juma'a ta makon da ya gabata, ya yi shellar sake nadin Boss Mustapha a matsayin sakataren gwamnatin Tarayya da kuma Abba Kyari, a matsayin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel