2019: Heineken Lokpobiri ya yi shirin fitowa takara a APC a Jihar Bayelsa

2019: Heineken Lokpobiri ya yi shirin fitowa takara a APC a Jihar Bayelsa

Tsohon karamin Ministan harkokin gona na Najeriya, Heineken Lokpobiri, ya tabbatar da shirinsa na tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar Bayelsa a zaben karshen shekarar nan da za a yi.

Sanata Heineken Lokpobiri ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamnan Bayelsa a karkashin jam’iyyar APC mai adawa a jihar. Lokpobiri ya sanar da Duniya wannan ne a ofishin APC.

Heineken Lokpobiri ya bayyana wannan ne a Ranar 13 ga Watan Yuni, 2019, lokacin da ya gana da jagororin APC na jihar Baylesa a babban ofishin jam’iyyar da ke hanyar Yenagoa zuwa Mbiama.

Za a gwabza be da tsohon Ministan noman kasar wajen samun tikitin APC a jihar ta Bayelsa, idan har ya yi nasara zai kara da PDP da sauran jam’iyyu wajen neman kujerar a cikin Watan Nuwamban bana.

KU KARANTA: Zaben Bayelsa: An ja dogon layi tsakanin Jonathan da tsohon Yaronsa

A Ranar Asabar, Lokpobiri ya ke fadawa shugabanin APC cewa:

“Na zo ne domin in sanar da ‘Yanuwan siyasana game da maganar niyyar tsayawa ta takarar gwamnan Bayelsa a karkashin jam’iyyar APC. Ina da jama’an da su taimaka mani lashe zaben 16 na Nuwamba.”

Mai shirin shiga takarar ya kara da cewa:

“Roko na shi ne in yi kira ga shugabannin jam’iyyar mu, su tsaya tsayin-daka wajen ganin mun hada-kai a wannan zabe domin mu yi nasara. Idan har mu ka hada-kai, babu shakka za mu yi nasara.”

Heineken Lokpobiri wanda ya taba yin Sanata a jihar ta Bayelsa, ya bayyana muradunsa na habaka tattalin arzikin jihar har ta kai ta tashi da kafafunta ba tare da dogaro da arzikin man fetur ba.

Shugaban APC na jihar watau Jothan Amos Esq ya ce za ayi adalci wajen tsaida ‘dan takarar jam’iyyar. A PDP akwai irin su Cif Timi Alaibe da Ambasada Godknows Igali da ke harin kujerar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel