Mamba a majalisar jihar Katsina, wasu mutane 8 sun mutu a hatsarin mota

Mamba a majalisar jihar Katsina, wasu mutane 8 sun mutu a hatsarin mota

Mamba mai wakiltar mazabar karamar hukumar Sabuwa a majalisar dokokin jihar Katsina, Mustafa Abdullahi, ya mutu sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da sh a kan hanyar Funtuwa zuwa Zaria ranar Juma'a.

Shaidun gani da ido sun ce motar dan majalisar kirar 'Hilux' ta yi 'taho mu gama' da wata mota da ta dauko yara daga kasuwa.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane a Kano, sun kubutar da yarinya mai shekara hudu

A cikin jawabin da ya fitar, mai magana da yawun majalisar, Nasiru Zango, ya ce kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Tasi'u Maigari, da ragowar mambobin majalisar 32 sun yi juyayin rashin marigayin tare da yi masa addu'ar Allah ya ji kansa.

Marigayi Abdullahi ya mutu ya na da shekaru 60 a duniya. An fara zabarsa zuwa majalisar dokokin jihar Katsina a shekarar 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel