Hukumar 'yan sanda ta cafke kwamandun Boko Haram 3 a Kano

Hukumar 'yan sanda ta cafke kwamandun Boko Haram 3 a Kano

Bayan da wata tawagar 'yan sanda ta musamman ta cafke wasu kasurguman masu ta'addancin garkuwa da mutane 3 a jihar Kano tare da kubutar da wata yarinya daga hannun su, hukumar 'yan sandan ta kuma cafke wasu kwamandu 3 na mayakan Boko Haram.

Hukumar 'yan sandan jihar Kano ta samu nasarar cafke wasu miyagun 'yan ta'adda 'yan kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram kamar yadda kwamishinan 'yan jihar Ahmed Iliyasu ya bayar da shaida.

Manyan 'yan ta'addan uku yayin shigar su hannu sun amsa laifin su tare da tabbatar da mukamin su na kasancewa kwamandun 'yan kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

A yayin da hukumar ta samun nasarar cafke daya daga cikin su a wani Otel dake unguwar Sabon gari, sauran biyun sun shiga hannu yayin wani simame da hukumar ta kai a wata maboyar su dake cikin birnin Kanon Dabo.

CP Iliyasu yayin gabatar da jawaban sa ga manema labarai ya ce akwai yiwuwar 'yan kungiyar 'yan ta'addan na yunkurin sake kafa dandazo a jihar Kano.

KARANTA KUMA: Za mu gina asibitoci masu cin gado 400 a sabbin masarautu 4 na Kano - Ganduje

A yayin da karshen alewa ya kasance kasa, Kwamishinan 'yan sandan ya yi bayanin cewa, daya daga cikin miyagun ababen ya yada zango ne a jihar Kano yayin da yake kan hanyar sa ta zuwa jihar Adamawa bayan ya taso daga babban birnin kasar nan Tarayya.

Kazalika hukumar 'yan sandan Kano ta samu nasarar kubutar da wata yarinya mai shekaru hudu, Khadijatu Rilwanu da aka yi garkuwa da ita a unguwar Na'ibawa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel