Hatsari: Rayuka 2 sun salwanta, mutane 9 sun jikkata a hanyar Ibadan zuwa Legas

Hatsari: Rayuka 2 sun salwanta, mutane 9 sun jikkata a hanyar Ibadan zuwa Legas

Hukumar kula da manyan hanyoyi FRSC reshen jihar Ogun, ta ce rayukan mutane biyu sun salwanta tare da jikkatar wasu mutane 9 yayin aukuwar wani mummunan hatsarin mota a garin Isara daura da babbar hanyar Ibadan zuwa Legas.

Shugaban reshen hukumar, Clement Oladele, shi ne ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai na kasa cikin garin Ota a ranar Lahadi 7, ga watan Yulin 2019.

Mista Oladele ya ce hatsarin da ya auku da misalin karfe 8.30 na ranar Asabar ya hadar da wata babbar motar dakon kaya da kuma wasu kananan motoci shida a yankin na Isara daura da babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Kwamandan hukumar ya alakanta wannan mummunan hatsari da sabawa ka'aidar tuki da kuma tsala gudu da ya wuce misali. Hatsarin da ritsa da mutane 35 ya salwantar da rayuka biyu yayin da mutane tara suka samu nau'ikan munanan rauni daban-daban.

Ya kuma gargadi direbobi da masu ababen hawa a kan kiyaye dukkanin dokoki da ka'idojin tuki tare da neman al'umma a kan gaggauta shigar da rahoton ko ta kwana ga hukumar a lambar wayar su ta 122.

KARANTA KUMA: Mamakon ruwan sama ya salwantar da rayuka 2, gidaje sun rushe a jihar Katsina da Kebbi

A baya cikin watan Yunin da ya gabata, makamancin wannan mummunan tsautsayi ya auku a kan wannan babbar hanya da ya ritsa da motoci bakwai yayin da rayukan mutane takwas suka salwanta gami da jikkatar mutane da dama.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel