Najeriya da Benin sun kulla muhimmiyar yarjejeniyar kasuwanci yayin taron AU a Nijar

Najeriya da Benin sun kulla muhimmiyar yarjejeniyar kasuwanci yayin taron AU a Nijar

Najeriya da Kasar Benin sun rattaba hannu a kan wata muhimmiyar yarjejeniya kulla kasuwanci a gaban shugabannin kasashe a dake halartar taron shugabannin kasashen Afrika (AU) da ake yi yau, Lahadi, a jamhuriyar Nijar.

An tafa wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da takwaransa na kasar Benin, Patrice Talon, a yayin da suka sa hannu a kan takardun kulla yarjejeniyar a taron da ke kan gudana a birnin Niamey, hedikwatar jamhuriyar Nijar, inda kuma za a kafa hedikwatar cibiyar kasuwanci da yarjejeniyar ta samar.

Najeriya ce kasar Afrika ta 53 da ta saka hannu a kan yarjejeniyar kasuwancin. Shugaba Buhari ya amince da shiga tsarin yarjejeniyar kasuwanci maras shinge bayan kwamitin da ya kafa domin nazarin tsarin ya mika masa rahotonsa.

Kwamitin ya bawa shugaba Buhari shawarar cewa shiga tsarin zai bunkasa tattalin arzikin Najeriya. Kazalika sun bayyana fargabar cewa tsarin kasuwancin maras shinge kan iya mayar da Najeriya jujin jibge kayayyakin da aka kera a kasashen da ba na Afrika ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel