Gwamnatin Kano ta bada kwangilar N730m domin yin gini a Asibitin Buhari

Gwamnatin Kano ta bada kwangilar N730m domin yin gini a Asibitin Buhari

-Gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai gina katafaren dakin kwantar da masu jinya mai dauke da gadaje 52 a Asibitin Kwararru ta Muhammadu Buhari dake Kano

-Naira miliyan 730 za'a kashe domin aiwatar da wannan aiki inda gwamnan ya sake fadin cewa a cikin mako mai zuwa za'a fara aikin gina cibiyar kula da ciwon daji duk a asibitin

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da kwangilar naira miliyan 730 domin ginin dankin kwantar da marasa lafiya mai dauke da gadaje 52 a Asibitin Kwararru ta Muhammadu Buhari dake babban birnin jihar.

Kwangilar ta ginin bene mai hawa daya za ta kunshi; dakunan malaman asibiti, ofis-ofis, dakin cin abinci da kuma dakin zama domin hutu.

KU KARANTA:Najeriya kasa ce mai fuska biyu ce, yayinda Kudu ke cigaba, Arewa na cibaya - El-Rufai

Da yake duba wurin da za’ayi ginin, gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya bada bayanin cewa, aikin dai an kirkire shi ne domin bai wa marasa lafiya kulawa, musamman masu fama da ciwon daji.

Gwamnan ya ce: “ A cikin aikin da za’ayi, zamu samar da cibiyar kulawa da masu cutar daji da kuma sashen dakunan kwantar da masu jinya wanda ya yi daidai da kundurin gwamnatinmu na samar da kyakkyawan yanayin kula da lafiya na musamman.”

Bugu da kari, gwamnan ya ce za’a kammala wannan aikin cikin watanni hudu zuwa biyar nan gaba, kuma zai sake daga darajar asibitin a fanni kayayyakin kula da lafiya.

“ Ina mai matukar farin ciki kasancewar wannan asibitin shi ne na farko a kasar nan da ya fara yin tiyatar kwakwalwa a duk asibitoci mallakar gwamnatin jiha a Najeriya. Asbitin ya samu gagaumar nasarar yi wa mutum guda tiyatar kashin baya kuma wanda shi ne karo na farko.” Inji gwamnan.

Da yake karin haske a kan cibiyar kula da ciwon dajin, Ganduje ya ce, a watan jiya ne aka bayar da kwangilar yin aikin, za’a fara aikin cikin mako mai zuwa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel