Kwallon kafa: Masar ta fatattaki Kocin ta, Mai horas da kasar Uganda ya ajiye aiki

Kwallon kafa: Masar ta fatattaki Kocin ta, Mai horas da kasar Uganda ya ajiye aiki

A lokacin da a ke cigaba da karawa a gasar cin kofin Nahiyar Afrika, an samu wasu kasashe da su ka raba gari da masu horas da manyan ‘yan wasanninsu. Wadannan kasashe su ne; Masar da Uganda.

Kasar Masar ta kori babban kocinta watau Javier Aguirre bayan an yi waje da kasar daga gasar bana. A jiya ne Kasar Afrika ta Kudu ta doke Masar daga gasar Nahiyar da ci daya tal mai ban haushi.

Wannan ne karon farko da Masar ta gaza tsallake zagayen farko a cikin shekaru 15 a gasar AFCON ta Nahiyar. Bugu da kari kuma wannan karo a na buga wannan wasanni ne a kasar ta Arewacin Afrika.

Kungiyar EFA ta kwallon kafan Masar ta tabbatar da cewa ta sallmi Koci Javier Aguirre da dukannin masu taya sa aiki. Shugaban EFA, Hany Abou-Rida, ya bada wannan sanarwa bayan an yi waje da kasar.

KU KARANTA: Super Eagles sun yi waje da Kamaru daga Gasar Afrika

Idan ba ku manta ba, an nada Aguirre ne bayan sakacin da kasar ta yi a Gasar cin kofin Duniya na bara inda a ka yi waje da ita a zagayen farko. A wancan lokaci Hector Cuper ne ya ke horas da ‘yan wasan.

Haka zalika kasar Uganda ta rabu da mai horas da ‘yan kwallonta watau Koci Sebastien Desabre. Kasar ta raba gari da kocin ne bayan duk sun cin ma yarjejeniyar hakan a Ranar 6 ga Watan Yulin 2019.

Sebastien Desabre ya ajiye aikin horas da ‘yan kwallon Afrika ta Gabas dinne bayan sun gaza isa rukuni na biyu na wannan gasa da a ke bugawa. An yi waje ne da Uganda daga Gasar ne a hannun Sanagal.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel