Gwamnonin da ke adawa da shirin 'Ruga' na son a cigaba da rikici ne - Miyetti Allah

Gwamnonin da ke adawa da shirin 'Ruga' na son a cigaba da rikici ne - Miyetti Allah

Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta kasa, 'Miyetti Alla Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN)', reshen jihar Nasarawa, Alhaji Mahammad Huseni, ya ce duk gwamnan da ke adawa da shirin gwamnatin tarayya na kasa 'Ruga' domin Fulani makiyaya ya na son a cigaba da rigingimu ne a jiharsa.

Huseni ya bayyana hakan ne yayin wata gana wa da ya yi da manema labarai a garin Lafia, babban birnin jihar Nasarawa, inda ya jaddada cewa kafa 'Ruga' a jihohin Najeriya 36 zai kawo karshen rikicin manoma da makiyaya da 'ya ki ci, ya ki cinye wa'.

Ya yi kira ga gwamnonin da ke nuna shakku a kan kaddamar da shirin kafa 'Ruga' da gwamnatin ktarayya ta bijiro da shi da su rungumi tsarin domin kawo karshen rigingimun da ke faruwa a jihohinsu.

Gwamnatin tarayya ce ta fara bullo da tsarin kafa 'Ruga' a dukkan jihohin kasar nan domin kawo karshen rikicin makiya da manoma.

DUBA WANNAN: Rashin lafiya: An yanke wa fitaccen jarumin fina-finan Hausa kafa daya (Hotuna)

Sai dai yanzu gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin biyo bayan suka da tirjewar da wasu gwamnonin jihohi, musamman na kudancin Najeriya, suka yi.

Amma duk da hakan wasu daga cikin gwamnonin arewacin Najeriya sun lashi takobin kaddamar da shirin a jihohinsu domin ganin cewa an ware wa Fulani makiyaya shingen kiwo, wanda yin hakan zai magance rikicin da ake samu tsakaninsu da manona.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel