Zaben Bayelsa: Dickson zai gamu da barazanar Magaji a PDP daga Jonathan

Zaben Bayelsa: Dickson zai gamu da barazanar Magaji a PDP daga Jonathan

A karshen shekarar nan ne za a shirya zaben gwamna a wasu Jihohi da su ka hada da Bayelsa da Kogi. A cikin farkon Watan Satumba ne jam’iyyar PDP za ta tsaida ‘yan takaran da za su yi zaben.

A jihar Bayelsa, Magoya bayan tsohon shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan da kuma wadanda ke tare da gwamna mai shirin barin-gadon mulki watau Seriake Dickson sun fara shiryawa wannan zabe.

Kowane bangare na ‘yan siyasar ya na kokarin ganin shi ne ya tsaida ‘dan takarar PDP, wanda kusan zai yi wahala bai lashe babban zaben da za a yi ba. PDP ta na karfi sosai a Kudu maso Kudancin kasar.

Goodluck Jonathan ne ya fara nada Seriake Dickson a gwamnati, a matsayin Kwamishinan sa lokacin ya na mulki, daga baya ya tafi majalisa, inda daga baya wata rigima da a ka yi ta sa ya zama gwamna.

Kamar yadda mu ka samu rahotanni daga jaridar Daily Trust, Goodluck Jonathan da Mai dakinsa watau Dame Patience Jonathan su na kokarin ganin yaransu ne su ka samu tikitin jam'iyyar PDP a zaben na bana.

KU KARANTA: Buhari ya sa hannu a kan kasafin kudin Birnin Tarayya

Gwamna Dickson mai shirin barin-gado da jama’arsa, sun nuna cewa ba za su yi na’am da wadanda Jonathan su ke so ba inda su ke zarginsu da cewa ba su cika ainihin ‘Ya ‘yan jam’iyyar PDP ba.

Mutanen Seriake Dickson su na ganin cewa wadanda Iyalin tsohon shugaban kasar su ke so su karbi mulkin jihar, su ne su ka jawo PDP ta rasa wasu mazabu a zaben 2019 a yankin Gabashin Bayelsa.

Dickson ya na da matukar karfi da ta-cewa a PDP ganin yadda na-kusa da shi su ka lashe kujeru a zaben 2019. Duk da haka Jonathan ta na shirin karawa da yaran gwamnan wajen ganin nasarar Reuben Okoya.

Rahotannin da mu ke samu sun nuna cewa yayin da a ke shirya zaben-gida na PDP, Okoya bai da farin-jini sosai a jihar Bayelsa, a dalilin kusancinsa da tsohuwar Uwargidar ta Najeriya, Dame Jonathan.

Sauran masu neman kujerar gwamnan a PDP sun hada da Cif Timi Alaibe da kuma Ambasada Godknows Igali. Duka wadannan ‘yan siyasa ba su cikin sahun yaran gidan gwamna Dickson.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel