Gabanin karewar wa'adin gwamnatin Buhari za mu yi kidayar al'ummar Najeriya - NPC

Gabanin karewar wa'adin gwamnatin Buhari za mu yi kidayar al'ummar Najeriya - NPC

Mukaddashin shugaban hukumar kidaya ta Najeriya, NPC, ya ce gwamnatin Tarayya za ta sake gudanar da kidaya a kan al'ummar Najeriya gabanin karewar wa'adin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a bisa kujerar mulki.

Yusuf Muhammad Anka, ya ce za sake gudanar da wata kidaya domin tabbatar da hakikanin adadin al'ummar kasar nan gabanin karewar wa'adi na biyu na gwamnatin shugaban kasa Buhari a kujerar sa ta jagoranci.

Mukaddashin shugaban hukumar NCP wanda kwamishinan hukumar reshen jihar Delta ya wakilta, Sir Richard Odibo, shi ne ya bayar da shaidar hakan a hedikwatar karamar hukumar Udu ta jihar Delta yayin kaddamar da shirin tantancewa na shiryen-shiryen kidaya na jihar.

Ya ce wannan shiri zai gididdiba kasar nan cikin yankuna daban-daban domin kawo sauki da kuma inganta harkokin gudanarwa yayin kidaya adadin al'ummar kasar nan da za a gudanar cikin tsawon shekaru hudu masu zuwa.

KARANTA KUMA: ASUU ta gargadi gwamnatin Najeriya a kan muhimmancin inganta harkokin ilimi

Ana iya tuna cewa hukumar NPC ta yi kidayar al'ummar Najeriya a shekarar 2006, inda aka samu adadin mutane 140,003,542 yayin da jihar Kano da kuma Legas suka kasance kan sahu na gaba ta fuskar yawan adadin al'umma.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel