Matsuguni: ‘Yan Majalisa su na neman bashi domin biyan kudin gida a Abuja

Matsuguni: ‘Yan Majalisa su na neman bashi domin biyan kudin gida a Abuja

Mun samu labari cewa wasu daga cikin ‘Yan Majalisa da-dama su na neman bashin kudi daga bankuna domin su iya biyan kudin hayar gidajen da za su zauna a babban birnin tarayya Abuja.

‘Yan majaliisar tarayyar za su karbi aron kudi a banki ne domin su magance matsalar wurin kwana kafin lokacin da za a biya su kudinsu. Za a biya kowane ‘dan majalisa akalla miliyan 65.

Kamar yadda mu ka samu labari, da zarar ayyuka sun kankama a majalisa, kowane ‘dan majalisa zai tashi da akalla Naira miliyan 65 zuwa miliyan 70, Wannan ita ce al’adar majalisa a Najeriya.

A na ba ‘yan majalisar wannan kudi ne domin sayen tufafi da motar hawa da neman wurin zama da sauran kayan cikin gida. Kawo yanzu wasu ‘yan majalisar kasar su na kwana ne a cikin otel.

KU KARANTA: Buhari ya sheka Jamhuriyar Nijar domin wani taron Afrika

Wani Sanata daga Kudancin kasar ya bayyanawa manema labarai cewa ya gaji da zama a otel don haka ya ke neman banki su ba shi aron kudi har ya iya biyan kudin hayar gida na shekara daya.

Sanatan ya ke cewa: “Dabarar da na ke shirin yi kafin a biya mu alawus shi ne in nemi aron kudi domin in saye fili kuma in kama gidan hanya na shekara guda cikin kwaryar Birnin Abuja”

“Na san cewa kafin karshen hayan da na kama, zan sa ido har in kammala gina gidan kai-na da zan shiga. Zan biya bashin da na karba da zarar alawus din mu sun fito.” Inji sabon 'Dan majalisar.

Sanatan ya bayyana cewa wani Abokin aikinsa ne wanda tuni ya gane dawar garin kuma ya yi nisa, ya kawo masa wannan shawara domin daina kashe makudan kudi wajen kwana a otel.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel