Akwai bukatar Buhari ya fara aikin dogon Kano zuwa Kaduna – Salihu Yakassai

Akwai bukatar Buhari ya fara aikin dogon Kano zuwa Kaduna – Salihu Yakassai

Yayin da a ka shiga wa’adi na biyu kuma na karshe na gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, wasu ‘yan kasar sun fara fitowa su na zayyana irin bukatunsu a gaban wannan gwamnati.

Daga cikin wadanda su ka bayyana na su muradun a fili akwai daya daga cikin babban Hadimin gwamnan jihar Kano mai suna Salihu Tanko Yakassai ya na mai nema a duba bukatun Arewa.

Salihu Yakkasai ya fito ya mika kokon baransa ga shugaban kasar ne a shafin sa na Tuwita a wani jawabi da ya yi a karshen makon nan. Ga kadan daga cikin abin da Salihu Yakassai ya rubuta:

“Barka da yamma shugaban kasa Buhari, kusan shekaru 2 kenan da su ka wuce ka bada umarni a soma aikin dogon jirgin kasa daga Jihar Kano zuwa Jihar Kaduna, amma har yanzu ba a soma aikin komai ba.”

Malam Salihu Yakassai ya kara da cewa:

“Haka zalika akwai batun aikin jawo gas zuwa Kano da a ka yi magana. Ya kamata shugaban kasa ya duba wadannan abubuwa a cikin kwanaki darin farkonsa a ofis a kan gadon mulki. Nagode!”

- @Dawisu

KU KARANTA: Babban Yaron Gwamnan Kaduna ya yi wa Buhari wata barazana

Tun tuni shugaban kasar ya yi alkawari za a jawo layin jirgin kasa daga Kano har Kaduna da kuma layin gas daga Ajaokuta har Kaduna zuwa Kano, amma kawo yanzu babu labarin wadannan ayyuka.

Yakassai ya na jin tsoron gwamnatin APC ta kammala wa’adin ta ba tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya duba mutanen Arewa ba. Yanzu dai Buhari ya na kan wa’adinsa ne na karshe.

Wasu da-dama dai sun ce lallai ya kamata Gwamnatin Buhari ta waiwayi Arewa inda wani Bawan Allah daga jihar ta Kano mai suna Ameenu Kutama ya maidawa Hadimin gwamna Ganduje martani cewa:

“Gaskiya dai, ya kamata mutane irinku su fito su rika magana tare da ba Mai gidan na ku shawara a game da wannan. Bai kamata mu rasa wadannan ayyuka ba, musamman aikin layin dogo.”

- @Ameenu_kutama

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel