Binciken 'Yan Sanda: Akwai yiwuwar a shiga kotu da Elisha Abbo a mako mai zuwa

Binciken 'Yan Sanda: Akwai yiwuwar a shiga kotu da Elisha Abbo a mako mai zuwa

Idan abubuwa su ka cigaba da tafiya a yadda su ke a yanzu, a na sa rai cewa a cikin makon nan da za a shiga ne Jami’an ‘yan sanda za su gurfanar da Elisha Abbo a gaban kotu da zargin laifi.

Za a maka Sanata Elisha Abbo a gaban kuliya ne bisa zargin kai wa wata Baiwar Allah hari a wani shago da a ke saida kayan manya. Wannan mummunan abu ya faru ne a Unguwar Wuse da ke Abuja.

‘Yan Sanda sun kammala bincike kuma su na daf da shigar da karar wannan Sanatan a kotu. Hakan na zuwa ne bayan an samu faifen bidiyon Sanatan ya na shararawa wannan Baiwar Allah mari.

Kamar yaddda mu ka samu labari, an shirya shiga kotu da sabon ‘dan majalisar tun a Ranar Juma’a, amma hakan bai yiwu ba saboda ba a gama tantance sahihancin faifen bidiyon da a ka samu ba.

KU KARANTA: ‘Yan Sanda sun bada belin Sanatan da ya wata Mata a shago

Jami’an tsaro su na kokarin tabbatar da ingancin wannan bidiyo ne a matsayin shaida domin gudun su gabatarwa Alkali faifen da a ka yi wa siddabaru, ganin irin girman wanda ake zargi da laifin.

A karshen makon da ya gabata, Rudunar ‘Yan Sanda sun tsare Sanatan na sa’a 24 inda su ka yi masa tambayoyi, har daga baya a ka bada belinsa tare da bukatar ya koma daga baya a cigaba da bincike .

Wani jami’in ‘yan sanda ya fadawa Manema labarai cewa su na bi sannu a hankali ne domin gudun a bar wani gibi a a shari’ar wanda ya na iya sa Sanatan ya samu kwararrun Lauyoyi su fitar da shi.

Idan ‘Yan Sanda sun kammala duk shirye-shiryen da a ke bukata, za su iya shigar da kara a farkon makon nan da za a shiga. Haka kuma majalisar dattawa a na ta bangaren, ta na gudanar da bincike.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel