Tsoron Allah: Matashi 'mai shara' ya mayar da gwal na miliyan N249 da ya tsinta

Tsoron Allah: Matashi 'mai shara' ya mayar da gwal na miliyan N249 da ya tsinta

An karramma wani matashi, mai shekaru 27, da ke aikin shara a kasar Dubai bayan ya mayar wa hukuma wata jaka da ke cike makil da gwal da ya fi na miliyan N249 da ya tsinta. Matashin ya dauki jakar zuwa ga hukuma ba tare da ya dauki wani abu daga cikin jakar ba.

Matashin mai suna Taher Ali ya bayyana cewa da farko ya dauka cewa jakar na dauke da karafan aikin kanikawa ne saboda nauyin karafan da ke cikinta.

An manta jakar ne a a wata kusurwa da ke gefe guda a filin ajiye motoci. Taher ya kula da jakar ne yayin da ya ke aikinsa na share-share.

Da Taher, dan asalin kasar Pakistan, ya daga jaka sai ya ji ta na da matukar nauyi, lamarin da ya sa shi yin mamakin abinda ke cikin jakar.

Tsoron Allah: Matashi 'mai shara' ya mayar da gwal na miliyan N249 da ya tsinta

Tsoron Allah: Matashi 'mai shara' ya mayar da gwal na miliyan N249 da ya tsinta
Source: Twitter

Tsoron Allah: Matashi 'mai shara' ya mayar da gwal na miliyan N249 da ya tsinta

An karrama matashi 'mai shara' da ya mayar da gwal na miliyan N249 da ya tsinta a Bubai
Source: Twitter

"Jakar na da matukar nauyi. Da farko na dauka jaka ce irin ta kanikawa don na yi zaton irin karamar akwatun nan ce mai dauke da irin karafaran da kanikawa ke tafiya aiki da su," Taher ya fada wa 'Gulf News'.

DUBA WANNAN: Gawa ta ki rami: Matashi Mohammed ya mike zumbur bayan an haka kabarun binne shi

Sannan ya kara da cewa: "mun ajiye jakar a gefe bisa tunanin mai ita zai dawo ya neme ta, musammam da muka ji ta na da matukar nauyi."

Daga baya ne daya daga cikin masu gadi da ke aiki a wurin ya bawa Taher shawarar cewa ya bude jakar ko zai ga bayanin wanda ya ajiye ta.

"Mun matukar girgiza da muka ga cewar gwal ne tari guda a cikin jakar, sai a lokacin mu ka fahimci dalilin nauyin jakar," a cewarsa.

Wadanda suka mallaki gwal din sun nuna jin dadinsu bisa yadda aka dawo musu da gwal dinsu na fiye da miliyan N249 ba tare da wani abu ya bata ba daga cikin jakar ba, lamarin da ya sa hukumomin kasar Dubai karrama Taher.

Source: Legit

Mailfire view pixel