Buhari ya yi martani kan nasarar da Super Eagles tayi akan Kamaru

Buhari ya yi martani kan nasarar da Super Eagles tayi akan Kamaru

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi martani akan nasarar da Super Eagles na Najeriya ta samu akan tawagar kungiyar Kamaru mai suna Indomitable Lions a yammacin ranar Asabar, 6 ga watan Yuli.

A wasan kwallon kafan ne Super Eagles ta ci Kamaru 3-2 wanda ya bata damar shiga matakin gaba na gasar cin kofin kasashen Afrika wato AFCON 2019.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya kungiyar Super Eagles murna akan nasarar da suka samu a gasar wanda ake yi a kasar Masar, bayan ta doke Kamaru.

Har ila yau Buhari ya yabi kwazo, hadin kai da jajircewa da yan wasan suka nuna a gasar, inda yace hakan alama ce da ke nuna daukakan kungiyar nan gaba.

Game da kalubalen da kungiyar zata fuskanta kafin tayi nasara, Shugaban kasar ya bukaci kungiyar da shuwagabanninta da su mayar da hankali tare da jajircewa, inda ya basu tabbacin samun goyon bayan yan Najeriya da kuma addu’oinsu.

Shugaban kasar ya wallafa sakon taya murna a shafinsa na twitter: “Muna taya Super Eagles murna. Mun jinjina wa kokarinku, hadin kai da kuma jajircewar ku. Kuna da cikakken goyon bayanmu akan wannan fafuta na daukaka."

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin da ke kin shirin Ruga na so a ci gaba da rikici – Miyetti Allah

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tawagar kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya ta samu nasara a kan tawagar Kamaru a gasar cin Kofin Kasashen Afirka na 2019 a kasar Egypt wanda aka fafata a yammain ranar Asabar, 6 ga watan Yuli.

Ga dukkan alamu fargabar da 'yan Najeriya suka nuna tun farkon fitowar jadawalin gasar wanda ya nuna alamun haduwar kasashen biyu duk da cewa rukunin kowacce daban, ta sa 'yan Super Eagles zama cikin shiri da ya kai su ga korar mai kambun gasar gida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel