AFCON: Najeriya ta fatattaki Kamaru zuwa gida

AFCON: Najeriya ta fatattaki Kamaru zuwa gida

Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya ta samu nasara a kan tawagar Kamaru a gasar cin Kofin Kasashen Afirka na 2019 a kasar Egypt wanda aka fafata a yammain ranar Asabar, 6 ga watan Yuli.

Ga dukkan alamu fargabar da 'yan Najeriya suka nuna tun farkon fitowar jadawalin gasar wanda ya nuna alamun haduwar kasashen biyu duk da cewa rukunin kowacce daban, ta sa 'yan Super Eagles zama cikin shiri da ya kai su ga korar mai kambun gasar gida.

Yanzu haka mai masaukin baki wato Egypt za ta fafata da Afirka ta Kudu kuma duk kasar da ta yi nasara to za ta kara da Najeriya a wasan dab da na kusa da karshe.

Kamaru wadda ita ce mai rike da kambu ta dauki kofin gasar sau biyar, inda ita kuma Najeriya ta dauka sau uku.

KU KARANTA KUMA: Ruga: Kungiyar Miyetti Allah ta nemi a bawa makiyaya Dajin Sambisa

Da fari dai dan wasan Najeriya, Odion Ighalo ya fara jefa kwallo a ragar Kamaru a minti 19 da fara wasan.

Amma dai sai gashi minti 20 bayan cin da Najeriya ta yi, sai aka samu yanayin da dan wasan Kamaru, Christian Bassogog ya wurga kwallo zuwa harabar Najeriya, inda shi kuma Stephane Bahoken ya zura ta a raga.

Mintuna uku bayan yin kunnen doki, sai tawagar Kamaru suka kara zura wa Super Eagles kwallo ta biyu ta hannun Clinton Njie.

Jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci dan wasan Najeriya, Odion Ighalo ya farke wa Najeriya, inda sakamako ya kasance 2-2.

Daga karshe sai Alex Iwobi ya jefa kwallo ta uku a ragar Kamaru.

A karshe dai Najeriya ta fattaki Kamaru gida bayan an tashi wasa 2-3.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel