Tsohon sojan Najeriya da yayi yakin duniya ya roki gwamnati ta biyashi fanshonsa

Tsohon sojan Najeriya da yayi yakin duniya ya roki gwamnati ta biyashi fanshonsa

-Tsohon sojan Najeriya mai shekaru 104 ya roki gwamnatin tarayya da ta biya shi fanshonshi

-Tsohon sojan ya bayyana cewa tun baya da aka sallameshi daga aikia cikin shekarar 1957 ba a taba biyanshi fansho ba

-Tsohon sojan ya bayyana haka ne a lokacin bikin ranar sojojin kasa na 2019

Wani tsohon sojan Najeriya mai shekaru 104 da yayi yakin duniya na biyu, Adamo Aduku, ya roki gwamnatin tarayya da ta biyashi kudin shi na fansho.

Aduku na daya daga cikin mutanen da aka ba kambun girmamawa na babban hafsun sojin kasa, a wajen bikin ranar sojojin kasa na 2019 da aka gudanar a jihar Legas.

Da yake magana da yan jarida a wajen taron, Aduku ya bayyana cewa an sallame shi daga aikin sojin kasa na Najeriya tun cikin shekarar 1957, amma yar yau bai taba karbar kudin shi na fansho ba.

Aduku ya bayyana cewa “Na shiga aikin soji na rundunar gidan sarauta na Afirika ta yamma a cikin shekarar 1942 a Markudi, jihar Binuwe. An bani horo a Laguna sa’annan a ka turani India a lokacin yakin duniya na biyu. Na yi yaki a Calacutta.

KARANTA WANNAN: Sarkin Gombe yayi kira ga mahajjatan jiharsa da kakkausar murya

Ya kara da cewa “Na sake shiga aikin sojin kasa a shekarar 1950 a Zariya daga nan ne aka sallame ni a cikin shekarar 1957”

“A yanzu haka ni manomi ne a Ibejukolo a karamar hukumar Omala dake a jihar Kogi.”

Ya kara da cewa “Ba a taba biya na fansho ba tun bayan da aka sallame ni. Ina rokan gwamnatin tarayya da ta duba lamari na don a samu a biya ni kudin na fansho.”

Oduku ya godewa rundunar sojin kasa ta Nageriya a bisa girmamamwar da akayi mashi.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel