Muhimman batutuwa 4 da suka yi fice a kasar a wannan makon

Muhimman batutuwa 4 da suka yi fice a kasar a wannan makon

Lamura da dama sun faru a kasar Najeriya a cikin wannan makon, don haka muka yi amfani da wannan fage wajen zakulo wasu muhimman batutuwa hudu da suka yi fice a fadin kasar.

Wadannan batutuwa dai sun ja hankalin jama’ar kasar da dama, inda wasu daga cikinsu suka janyo cece-kuce na tsawon lokaci.

Ga batutuwan kamar haka:

1. Marin wata mai jego da Sanata Elisha Abbo yayi

Lamarin mari da ake zargin Sanata Elisha Abbo, wanda ke wakiltar shiyyar arewacin jihar Adamawa yayi wa wata mai jego da ke jiran wani shagon siyar da kayan jima’i ya dauki hankalin jama’a dama a kasar ciki harda yan siyasa.

Mutane da dama sun yi tir da wannan abu da ake ganin sanatan ya aikata bayan bayyanar bidiyon faruwar al’amarin.

2. Buhari ya dakatar da batun kirkirar Rugar Makiyaya

Bayan cece-kuce da aka tayi tsakanin gwamnonin jihohi, Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa ta dakatar da shirinta na kirkirar Rugar makiyaya.

Hadimin Shugaba Muhammadu Buhari kan kafafen sadarwa na zamani Bashir Ahmad ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na Twitter.

Hakan dai yayi wa wasu mutane da dama dadi domin dama tun farko mafi akasarin mutane sun nuna adawarsu akan wannan shiri na gwamnatin tarayya.

3. Yadda aka ceto surukin dogarin Buhari a Kano

A ranar Talata ne Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kubutar da Magajin Garin Daura Aljahi Musa Umar wanda wasu 'yan bindiga suka dauke watanni biyu da suka wuce.

Runduna ta musamman da ke yaki da masu garkuwa da mutane wato Operation Pupp Adr karkashin jagorancin Abba Kyari tare da hadin gwiwar rundunar 'yan sandan Kano ne suka kubutar da magajin garin.

Alhaji Musa Umar dai, surukin dogarin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne.

KU KARANTA KUMA: Sarkin Gombe yayi kira ga mahajjatan jiharsa da kakkausar murya

4. Shugaba Buhari yayi nade-naden mukamai

A cikin makon nan ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi nade-naden wasu mukamai a gwamnatinsa.

Daga cikin nade-naden Shugaban kasar, ya sake dawo da Boss Mustapha a matsayin babban sakataren gwamatin tarayya tare da Abba Kyari a matsayin Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa a karo na biyu.

Haka zalika shugaba Buhari ya nada hadimansa guda 11.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel