Sarkin Gombe yayi kira ga mahajjatan jiharsa da kakkausar murya

Sarkin Gombe yayi kira ga mahajjatan jiharsa da kakkausar murya

Sarkin Gombe kuma Amirul Hajji na jihar, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, ya yi kira ga mahajjata daga jihar da su kasance masu bin ka’idoji da matakan da ke tattare da aikin Hajji har zuwa lokacin da za su kammala aikinsu.

Sarkin ya bayyana hakan ne a bikin kulle horas da mahajjata daga jihar Gombe.

Ya kuma bukaci mahajjatan sun zamo masu bin dokar kasar Saudiyya a tsawon lokacin da za su kwashe a kasar mai tsarki suna ibada.

“Ku kwana da sanin cewa za ku je wata kasa ce da ta sha bambam da naku kasar. Don haka, muna neman hadin kanku domin yin aikin hajji mai cike da nasara,” inji shi.

Sarki Abubakar III ya ce tawagar Amirul-Hajj na jihar sun shirya tsaf domin tabbatar da gudanawar hajjin 2019 ya tafi daidai, cewa an fara shirye-shiryen cikin nasara.

A nashi jawabin, wani mamba na tawagar Amirul Hajji, Sheikh Adamu Muhammad Dokoro ya bukaci mahajjatan da su mutunta shugabanninsu, suyi watsi da yada jita-jita da kuma tattauna abubuwan ki a tsakaninsu a lokacin aikin hajji.

KU KARANTA KUMA: Kurunkus: Magana ta canja akan zuwan mawakiya Nicki Minaj Saudiyya - Sheikh Kabir Gombe

A nashi bangaren, babban sakataren kungiyar alhazai, Alhaji Sa’adu Hassan ya yi kira ga mahajjata da su kasance jakadu nagari na jihar dama kasa baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel