Assha: Uwargida ta jibgi Maigida har lahira

Assha: Uwargida ta jibgi Maigida har lahira

A kullun abubuwan ban-al’ajabi da mamaki na ci gaba da faruwa a tsakanin mutanen wannan karni, har ta kai a yanzu zaman lafiya yayi karanci a tsakanin ma’aurata harma da wadanda suka yi auran soyayya.

A baya-bayan nan an samu lamura da dama wanda ke nuna inda mata ke sheka mazajensu lahira sakamakon sabani kowani rashin jituwa da ke gibtawa a tsakaninsu.

Hakan ne ya faru a tsakanin wasu ma’aurata a yankin Darmnawa bayan gandun Sarki a birnin Kano, inda muka ji cewa wata uwargida ta yi ajalin maigidanta sakamakon rashin jituwa da ya gibta a tsakaninsu.

Wani mai amfani da shafin Facebook, Ahmad Deedat ne ya wallafa labarin, inda yace rikici ne ya fara kaurewa tsakanin matar da makwabtansu akan fadan yayansu, ana cikin haka ne sai mijin ya dawo ya tarar dasu.

Sai dai ba tare da bata lokaci ba mijin ya kora yaransa gida tare da matar tasa, sa’annan ya baiwa makwabtan hakuri. haka ta shirya masa mugunta. Sai dai hakan da maigidan yayi bai mata dadi ba saboda haka ta kulla masa wani tuggu.

KU KARANTA KUMA: Kurunkus: Magana ta canja akan zuwan mawakiya Nicki Minaj Saudiyya - Sheikh Kabir Gombe

Yana shiga gida ta dauki wani katako ta rafka mashi ba kakkautawa har ya yanke jiki ya fadi matacce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel