Buhari ya tashi daga Abuja zuwa Nijar domin halartar taron AU

Buhari ya tashi daga Abuja zuwa Nijar domin halartar taron AU

-Shugaba Buhari ya bar Abuja ranar Asabar zuwa Nijar inda zai halarci taron kasuwanci na kasashen Afirka

-Taron na wannan shekara shi ne karo 12 inda za'a kaddamar da sabon tsarin kasuwanci maras shinge na Afirka wanda aka sanya wa taken 'AfCTA'

Shugaba Muhammadu Buhari ya bar Babban Birnin tarayyar Abuja a ranar Asabar zuwa kasar Nijar inda zai halarci taron AU a Yammai.

Shugaban kasan ya shilla zuwa kasar Nijar a safiyar ranar Asabar inda zai hade da takwarorinsa na sauran kasashen Afirka.

KU KARANTA:An kama wata mata na zina da wanda ya kashe mijinta

Mun samu labarin tashin Buhari ne a wani sako da Fadar Shugaban Najeriya ta fitar ta hanyar amfani da shafinta na Tuwita @AsoRock.

Yayin wannan ziyara ana sa ran, Shugaba Buhari zai halarci taron AU wanda zai mai da hankali a kan maganar kasuwancin Nahiyar Afirka gaba daya. A jerin ire-iren wadannan taron wannan shi ne karo na 12.

Har ila yau, zaman na Gamayyar kasashen Afirka zai kaddamar da sabon tsarin kasuwanci domin kasashen Afirka wanda aka sanya wa taken ‘African Continental Free Trade Area (AfCTA)’ wato kasuwanci maras shinge.

Daga cikin abubuwan da wannan sabon tsarin kasuwancin maras shinge da za’a kaddamar ya kunsa akwai bude shafin intanet na musamman domin kula da tsarin, hanyar biyan kudi ta zamani da kuma bangaren lura da abinda ke gudana.

Gabanin halartar wannan taron sai da Shugaba Buhari ya tuntubi masana da kuma kwararru a Najeriya kan harkar kasuwanci san nan daga baya ya amince da cewa Najeriya zata kasance cikin yarjejeniyar.

Shugaba Buhari zai rattaba hannu bisa takardar yarjejeniyar AfCTA a Yammai inda AU za ta gudanar da taron na ta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel