Hukumar yaki da almundahana za ta binciki yadda ake biyan ma’aikatan jihar Kano albashi

Hukumar yaki da almundahana za ta binciki yadda ake biyan ma’aikatan jihar Kano albashi

-Hukumar yaki da almundahana ta jihar Kano ta bayyana cewa za ta binciki yadda ake biyan ma'aikatan jihar albashi

-Barista Muhuyi ya bayyana cewa binciken ya zama dole duba da yadda wasu ma'aikata ke ganin ana tura masu kuidade masu yawa akan albashinsu

Shugaban hukumar sauraron koken al’umma da yaki da rashawa ta jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce hukumar za ta binciki yadda ake biyan ma’aikatan jihar albashi.

Barista Muhuyi Magaji ya bayyana cewa suna zargin akwai wata makarkashiya dake gudana a wajen yadda ake biyan ma’aikatan jihar Kano, saboda haka akwai bukatar a binciki lamarin.

Barista muhuyi ya bayyana cewa hukumar ta gano akwai ma’aikatan jihar da ake biya kudade fiye da albashinsu a yan kwanakin nan.

Ya bayyana cewa “Kwanan nan wata mata dake aiki da hukumarmu ta ga an turo mata albashi fiye da Naira 400,000 akan albashinta.”

Ya kara da cewa “Haka zalika, wani ma’aikacin mu da ke aiki a karamar hukumar Gezawa ya ga an turo mashi karin albashi. Dukka ma’aikatan biyu sun mayar da karin da akayi masu zuwa ga asusun gwamnati.”

KARANTA WANNAN: Yan sanda sun yi fata-fata da yan ta’adda sun ceto mutane da dama

Barista Muhuyi ya bayyana cewa baya ga wadannan, hukumar su ta samu labari cewa wasu ma’aikatan ministirori da hukumomin gwamnati na ansar karin kudi fiye da albashinsu. A saboda haka akwai bukatar a binciki lamarin.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa dole sai sun binciki lamarin saboda basu sani ba ko akwai wata makarkashiya cikin karin kudin da ake baiwa ma’aikata akan albashinsu.

Daga karshe yayi kira ga yan Najeriya da su baiwa hukumomin hana cin hanci da rashawa goyan baya don magance annobar cin hanci da rashawa.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel