Ruga: Kungiyar Miyetti Allah ta nemi a bawa makiyaya Dajin Sambisa

Ruga: Kungiyar Miyetti Allah ta nemi a bawa makiyaya Dajin Sambisa

Bayan jingine shirin samar da rugar makiyaya da gwamnatin tarayya tayi a kwana-kwanan nan sakamakon cece-kuce da aka rika yi kan batun, Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Kautel Horre na Kasa, Alhaji Abdullahi Bodejo ya roki gwamnatin tarayya ta bawa makiyaya Dajin Sambisa.

Bodejo ya shaidawa The Sun cewa Fulani ba su bata neman a samar musu da ruga ba tun farko, ya dai ce ne kawai suna bukatar a samar musu da kayayakin da suke bukata ne domin su koma sabon wurin.

Ya ce: "Ko a Dajin Sambisa ko ma ina ne, Fulani za su iya zama. Fulani ba su tsoron Dakin Sambisa ko wata dajin. Fulani za su iya zama a ko wane daji idan dai akwai ruwa da ciyayi da dabobinsu za su ci. Idan Sambisa na da wadannan abubuwan, ba sai an nunawa fulani ba, za su kora shanunsu su tafi can.

DUBA WANNAN: An gano yarjejeniyar da aka kula tsakanin Goje da Shugaba Buhari kafin ya janye takararsa

"Idan dai ka ga Fulani suna gudun wani wuri, toh babu ruwa da ciyayi ne. Idan fulani ba su tafi wurare kamar Enugu, Benue da Taraba ba, ba za a samu kasar noma mai kyau ba, babu wanda zai iya noma a wurin.

"Fulani sun fara zama a wurare da dama har da babban birnin tarayya kafin manoma su zo wurin. Saboda haka idan gwamnatin tarayya za ta mallakawa fulani Sambisa, zamu tafi can. Ni ne mutumin farko da zan tafi.

"Babu wanda ya ce yana son ruga. Fulani suna da rugar su. Ba dai wuri ne kawai da fulani ke da gina gidajensu ba? Saboda haka muna da ruga amma ban san abinda ya janyo matsala ba akan harkokin fulani a kasar nan. Muna da wuraren kiwo da aka killace mana amma mutane ba su magana. Da farko sun ce filayen kiwon shanu za a kafa yanzu kuma an ce Ruga."

Shugaban na Miyetti Allah ya ce babu wanda ya tuntube su kan batun yadda za a shawo kan matsalar. Ya ce wasu ne kawai ke zuwa wurin gwamnati da sunan shugabanin fulani suna karbar kudi. Ya ce idan da gaske ake yi a zo a same su a tattauna domin shawo kan matsalar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel