Dan majalisar da APC ta dakatar ya mayar mata da martani

Dan majalisar da APC ta dakatar ya mayar mata da martani

Dan majalisar jihar Edo na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Mista Chris Okaeben ya yi korafi kan dakatar da shi da jam'iyyar tayi a karamar hukumar Oredo na jihar Edo saboda saba dokokin jam'iyyar.

Okaeben yana daya daga cikin 'yan majalisa 16 cikin 24 da aka ki gayyata rantsar da shugabanin majalisar jihar ba da aka gudanar a ranar 17 ga watan Yuni saboda adawa da ya ke yi da zabin Mista Frank Okiye wanda na hannun daman Gwamna Godwin Obaseki ne.

A jawabin da dan majalisar ya yi jiya Juma'a a Benin ya ce shugabanin jam'iyyar na karamar hukumarsa ba su da ikon dakatar da shi.

DUBA WANNAN: Tirkashi: Dan El-Rufai ya yi wa Buhari barazana kan nadin sabbin ministoci

Ya ce, "Shugabanin jam'iyya na jiha ne kadai ke da ikon dakatar da ni kuma dole sai sun samu amincewar Kwamitin Gudanarwa na Jam'iyyar wato NWC. Martin Osakwe da ya sauya sheka daga PDP ya shigo APC bai san yadda dokokin jam'iyyar su ke bane."

Da farko,an bawa Okaeben wa'addin kwanaki biyu ya nemi afuwar Gwamnan jihar Godwin Obaseki saboda rashin biyaya da ake zarginsa da aikatawa amma ya ce ba zai aikata hakan ba saboda babu laifin da ya yi.

Godwin Alabi, Ciyaman din APC a karamar hukumar Oredo ya ce dan majalisar ya sabawa sashi na 21 na kundin dokokin APC wanda ya tanadi ladabtarwa da za a yi wa mambobin jam'iyyar da su kayi laifi.

Ya ce Okaeben ya ki amsa gayyatar da akayi masa domin sauraron korafin da ya ke da shi kan jam'iyyar.

"Bayan maganganun da ya furta, Shugabannin jam'iyyar APC na karamar hukumar sun bukaci ya bayar da hakuri amma ya ki biyaya ga umurnin jam'iyyar a maimakon hakan ya yi barazana ga rayuwar shugaban jam'iyyar na karamar hukumar, Godwin Alabi," inji shi.

Ciyaman din APC na karamar hukumar Oredo, Mr Jenkins Osunde ya ce, "Jam'iyya ta riga da dauki mataki kan Chris Okaeben" kuma ya bukaci sauran 'yan jam'iyyar su mayar da hankula kan marawa Gwamna Godwin Obaseki baya domin ya yi wa mutanen Edo aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel