Gini ya rufto akan wasu yara 2 sakamakon guguwar iska da ta taso a jihar Katsina

Gini ya rufto akan wasu yara 2 sakamakon guguwar iska da ta taso a jihar Katsina

Wata guguwar iska mai karfi da aka yi a daren ranar Alhamis yayi sanadiyar mutuwar yara biyu da kuma lalata akalla gidaje 70 a karamar hukumar Jibia da ke jihar Katsina.

Wasu idon shaida sun bayyana cewa lamarin ya fara ne da tsakar dare sannan ya kwashe tsawon sama da mintuna 30 yana kadawa.

Yankunan da lamarin ya shafa sosai sun hada da Sabuwar Unguwar Gadrige da kuma Unguwar Malamai.

Wani matashi dan shekara 13, Usman Jafar da wani kuma da ba a bayyana sunansa ba ne suka mutu sakamakon ruftowa da gini yayi a kansu.

Jaridar Daily Trust ta ruwait cewa tuni dai aka yi jana’izar yaran.

KU KARANTA KUMA: Kurunkus: Magana ta canja akan zuwan mawakiya Nicki Minaj Saudiyya - Sheikh Kabir Gombe

A wani labari na daban, mun ji cewa hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta jero wasu jihohi da kananan hukumomin kasar da cutar amai da gudawa zai addaba idan ba a dauki mataki ba.

Hukumar ta gano haka ne a bincike da ta kaddamar da tare hadin guiwar ‘eHealthAfrica’ inda ta bayyana cewa jihohin Kano, Kebbi da Sokoto na cikin wadanda za su yi fama da wannan matsala idan ba ayi gaggawan daukan mataki a kai ba.

NCDC ta ce sakamakon wannan binciken zai taimaka wajen fadakar da gwamnatocin jihohin kasar nan wajen maida hankali game da cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel