Yanzu yanzu: Masu garkuwa da mutane sun sako likitan Kano bayan da aka biya miliyoyin kudi

Yanzu yanzu: Masu garkuwa da mutane sun sako likitan Kano bayan da aka biya miliyoyin kudi

-An sako wani likita mazaunin Kano bayan da aka yi garkuwa dashi a ranar Laraba 3 ga watan Yuli 2019

-An sace Dr. Bashir tare da yan uwansa guda uku akan hanyarsu ta zuwa Okene

-Majiya ta bayyana cewa an sako Dr. Bashir bayan da aka biya kudin fansa Naira miliyan 10

An sako Dr. Bashir Zubayr, likita mazaunin jihar Kano da aka sace tare da yan uwansa guda uku akan titin gwamnatin tarayya na Lokoja zuwa Okene a ranar Laraba 3 ga watan Yuli 2019.

Majiya a cikin dangin likitan da ta bukaci a sakaye sunanta ta bayyana cewa an saki likitan da yan uwan nashi da marecen ranan Juma'a bayan da aka biya kudin fansa Naira miliyan 10.

Majiyar ta bayyana cewa aranar Alhamis 4 ga watan Yuli masu garkuwa da mutanen sun tuntubi dan uwan likita, Hamza Zubairu inda suka nemi kudin fansa Naira miliyan 200.

Shugaban kungiyar likitoci reshen jihar Kano, Sanusi Bala ya bayyana cewa an sanar da kungiyar ta kasa game da afkuwar lamari.

KARANTA WANNAN: LABARAISIYASA 2023: Tinubu ne ya fi cancanta ya shugabanci Najeriya - Kungiya

Sanusi Bala ya kuma bayyana cewa kungiyar ta tuntubi iyalan likitan da akayi garkuwan da shi kuma za su yi iyakar kokarinsu don ganin an sako shi.

A ranar Laraba 3 ga watan Yuli 2019, Legit.ng ta ruwaito cewa masu garkuwa da mutane sun dauke wani dakta Bashir Zubayr tare da kannansa maza guda biyu da kanwarsa mace guda a Irepeni, kilomita 20 a yamma daga garin Lokoja.

An bayyana cewa Dr. Bashir Zubayr na kan hanyar zuwa Okene wajen sadakar 40 na rasuwar mahaifyarsu.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel