Buhari ya rattafa hannu a kasafin kudi na babban birnin tarayya

Buhari ya rattafa hannu a kasafin kudi na babban birnin tarayya

-Shugaba Buhari ya amince da kasafin kudi na babban birnin tarayya da majalisa ta takwas ta zartar

-Haka zalika, shugaba Buhari ya amince da kudirin samar da makarantar Poly a karamar hukumar Daura ta jihar Katsina

-Mai taimakawa shugaba Buhari kan harkokin majalisa, sanata Ita Enang ne ya bayyana hakan

A jiya Juma’a 5 ga watan Yuli, 2019, shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu a kasafin kudi Naira biliyan 243.374 na babban birnin tarayya na shekarar 2019.

Majalisar tarayya ta 8 da ta shude ne ta zartar da kasafin kudin na babban birnin tarayya kafin wa’adin mulkinsu ya kare.

Shugaba Buhari ya kuma rattafa hannu a kudirin da majalisa ta kai na samar da makarantar poly ta gwamnatin tarayya a Daura dake a jihar Katsina.

Babban mai taimakawa shugaba Buhari akan harkokin majalisa (Majalisar Dattawa), sanata Ita Enang ya bayyana cewa shugaban kasa Buhari ya rattafa hannu a kudirorin guda biyu da majalisa ta takwas ta zartar.

A ranar Alhamis 3 ga watan Yuli 2019, Legit.ng ta ruwaito cewa shugaba Muhammadu Buhari ya ki amincewa da kudirori 17 da majalisar Najeriya ta takwas ta zartar.

KARANTA WANNAN: 2023: Tinubu ne ya fi cancanta ya shugabanci Najeriya - Kungiya

A ranar Alhamis din dai, sanata Ita Enang ya bayyana ma manaima labarai cewa shugaba Buhari ya amince da kudirori tara na majalisar amma ya ki amincewa da guda 17.

Daga cikin kudirorin da shugaba Buhari yaki amincewa da su, sun hada da: kudirin samar da jami’ar gwamnatin tarayya ta karatun koyarwa a Kano, da kudirin samar da jami’ar gwamnatin tarayya ta karatun koyarwa a Zariya

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel