Nadin mukamai: Ba muyi mamakin hanamu kujerar SGF ba, inji Ohanaeze

Nadin mukamai: Ba muyi mamakin hanamu kujerar SGF ba, inji Ohanaeze

-Kungiyar Ohanaeze ta ce sam ita rashin ba wa inyamuri mukamin Sakataren Gwamnatin Tarayya bai ba ta mamaki ba

-Kakakin kungiyar ne ya bada wannan bayani ranar Asabar yayin da yake zantawa da 'yan jarida a Abuja

-Kafin Shugaban Buhari ya sake nada Boss Mustapha bisa wannan kujera anyi ta hasashen tsohon minista kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu a matsayin wanda za'a ba mukamin na SGF

Yankin Kudu maso Gabas na Najeriya ya rasa samun kujerar Sakataren Gwamnatin Tarayya wato SGF, bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya sake nada Boss Mustapha kan kujerar.

Yankin na jihohin Inyamurai dake Kudancin Najeriya ya kasance kafin wannan nadin yana hasashen cewa za’a bai wa Ogbonnaya Onu, tsohon ministan kimiyya da fasaha wannan kujera.

KU KARANTA:An kama wata mata na zina da wanda ya kashe mijinta

Onu, wanda ya fito daga jihar Ebonyi ya kasance cikin jam’iyyar APC wadda ta tsayar da Buhari a matsayin dan takarar Shugabancin kasa har sau biyu.

A halin yanzu da aka riga aka cike mukaman Shugaban kasa, mataimakinsa, shugabannin majalisar dokoki da mataimakansu, ta tabbata cewa yankin Kudu maso Gabas bata da babban muqami ko daya.

A lokacin wa’adinsa na farko, Sanata Ike Ekweremadu ne ya samu nasarar zama mataimakin shugaban majalisar dattawa abinda bai wa ‘yan APC dadi ba. A halin yanzu kuwa, Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa shi ne mafi girman mukami da inyamuri yake rike da shi.

Da yake zantawa da wakilin jaridar Punch a ranar Asabar, Kakakin kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Mista Uche Achi-Okpaga, ya ce, “ tunda Kudu maso Gabas ta rayu tsawon wa’adin Buhari na farko a yanzu ba za mu mutu ba.”

Achi-Okpaga ya cigaba da cewa: “ Sam mu ba muyi mamakin wannan lamari ba. Wannan ma ai ba wani labarin fadi bane. Dama can ba muyi tsammanin wani abu daga wajensa ba tun ranar da aka rantsar da shi a karo na biyu.

“ Tun a wa’adin farko na mulkinsa yake nuna mana bangaranci. Tunda har Allah yasa mu kayi wa’adin farko ba tare da mun mutu ba, yanzu ma ba za mu mace ba saboda an hanamu mukami.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel