NAF ta yabawa Buhari a kan kulawar da yake bai wa jami’anta

NAF ta yabawa Buhari a kan kulawar da yake bai wa jami’anta

-Hafsun sojin saman Najeriya Abubakar Sadiq ya mika godiyarsa ga Shugaba Buhari bisa kulawar da yake ba wa rundunar sojin saman

-Sadiq ya fadi wannan jawabin ne a wurin wata liyafa da rundunarsa ta shirya a jihar Bauchi ranar Juma'a

-Sakataren gwamnatin jihar Bauchi Muhammad Baba shi ne ya wakilci gwamnan jihar inda ya nemi dakarun sojin saman da su cigaba da dagewa wurin sama wa kasar nan tsaro mai inganci

Rundunar sojin saman Najeriya wato NAF ta yabawa Shugaba Buhari a kan irin kulawar da yake bai wa dakarunta musamman wurin samar masu da horo a fadin kasar.

Hafsun sojin saman Najeriya, Sadiq Abubakar ne ya fadi wannan zancen a wurin wata liyafa da bangaren ayyuka da horo na musamman na rundunar sojin ya shirya a Bauchi ranar Juma’a.

KU KARANTA:An kama wata mata na zina da wanda ya kashe mijinta

Abubakar ya nuna jin dadinsa bisa kulawar da Shugaba Muhammadu Buhari yake ba wa Rundunar sojin saman ta bangaren bayar da horo da kuma sauran bukatun dakarunsu.

A cewarsa, taimakon da gwamnatin tarayya ta kasance tana bai wa rundunar ya matukar taimakawa wajen kawo sauye-sauye a harkokinta.

Bugu da kari, hafsun sojin ya tabbatar wa shugban kasan cewa, dakarunsa ba za suyi kasa a gwiwa ba wajen yin aikin da zai fidda kasar nan daga cikin halin firgicin da take na rashin tsaro.

Haka zalika, Sadiq Abubakar, ya miqa sakon godiya ga gwamnatin Jihar Bauchi bisa irin goyon bayan da take ba su tare da ilahirin jama’an jihar.

Ga abinda ya fadi a kalaman nasa: “ Bari in yi amfani da wannan damar domin in miqa godiyata ga gwamnati da kuma al’ummar Jihar Bauchi bisa goyon bayan da suke bamu daga bangarensu wurin tabbatar da kasar nan ta samu tsaron da ya dace.”

A nashi jawabin, Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad wanda sakatare gwamnatin jihar ya wakilta, Muhammad Baba, ya roki NAF da ta cigaba da jajircewa yayin gudanar da ayyukanta na samar da tsaron kasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel