Edo: An dakatar da dan majalisar jam'iyyar APC saboda rashin da'a

Edo: An dakatar da dan majalisar jam'iyyar APC saboda rashin da'a

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a karamar hukumar Oredo na jihar Edo ta dakatar da zababen dan majalisar jihar mai wakiltan mazabar Oredo Ta Yamma, Chris Okaeben.

An sanar da dakatarwar ne a ranar Juma'a 5 ga watan Yuli a wurin babban taron mambobin jam'iyyar da aka gudanar a karamar hukumar.

Dan majalisar yana daya daga cikin wadanda suka tubure cewa ba a bi ka'ida ba wurin zaben shugabanin majalisar jihar Edo zubi na bakwai.

DUBA WANNAN: An gano yarjejeniyar da aka kula tsakanin Goje da Shugaba Buhari kafin ya janye takararsa

An bawa Okaeben wa'addin kwanaki biyu ya nemi afuwar Gwamnan jihar Godwin Obaseki saboda rashin biyaya da ake zarginsa da aikatawa amma ya ce ba zai aikata hakan ba saboda babu laifin da ya yi.

Godwin Alabi, Ciyaman din APC a karamar hukumar Oredo ya ce dan majalisar ya sabawa sashi na 21 na kundin dokokin APC wanda ya tanadi ladabtarwa da za a yi wa mambobin jam'iyyar da su kayi laifi.

Ya ce Okaeben ya ki amsa gayyatar da akayi masa domin sauraron korafin da ya ke da shi kan jam'iyyar.

"Bayan maganganun da ya furta, Shugabannin jam'iyyar APC na karamar hukumar sun bukaci ya bayar da hakuri amma ya ki biyaya ga umurnin jam'iyyar a maimakon hakan ya yi barazana ga rayuwar shugaban jam'iyyar na karamar hukumar, Godwin Alabi," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel