2023: Tinubu ne ya fi cancanta ya shugabanci Najeriya - Kungiya

2023: Tinubu ne ya fi cancanta ya shugabanci Najeriya - Kungiya

- Wata kungiyar siyasa a jihar Osun, The Ifesowapo Society ta ce Aiswaju Ahmed Bola Tinubu ya cancani ya jagoranci Najeriya a 2023

- Shugaban kungiyar, Samuel Jegede ya yi bayyanin cewa Tinubu taka muhimmiyar rawa don ganin Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa

- Sai dai wani jigo a Kungiyar Arewa Consultative Forum, Mohammed Abdulrahman ya ce Tinubu ba zai iya darewa kan mulki ba bayan Buhari ya kammala wa'adinsa

Kungiyar siyasa ta mai suna 'The Ifesowapo Society' da ke Osun ta ce jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya cancanci zama shugaban kasa idan za a mayar da mulki yankin Kudu a 2023.

A jawabin da shugaban kungiyar, Samuel Jegede ya yi a babban birnin jihar Osogbo, ya ce goggewa da muhimman abubuwan da Tinubu ke yi a siyasar Najeriya kawai ya isa zama hujja.

DUBA WANNAN: An gano yarjejeniyar da aka kula tsakanin Goje da Shugaba Buhari kafin ya janye takararsa

The Nation ta ruwaito cewa Jegede ya ce muhimmiyar rawar da Tinubu ya taka domin ganin Shugaba Buhari ya zama shugaban kasa ba zai misaltu ba.

Ya ce yankin Kudu Maso Yamma ta dade tana fitar da goggagun 'yan siyasa tun zamanin rusheshiyar Yankin Yamma lokacin da fitaccen dan siyasa, Obafemi Awolowo ya zama zakaran gwajin dafi a siyasa.

A wani rahoton, Legit.ng ta ruwaito cewa wani jigo a Kungiyar Arewa Consultative Forum, Mohammed Abdulrahman ya ce ba zai yiwu Tinubu ya karbi mulki a 2023 bayan karewar wa'addin Buhari ba.

Abdulrahman wanda mai nazarin al'amurran siyasa ne ya ce babu yadda za ayi wani Kirista daga kudancin Najeriya ya zama shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel