Yan sanda sun yi fata-fata da yan ta’adda sun ceto mutane da dama

Yan sanda sun yi fata-fata da yan ta’adda sun ceto mutane da dama

-Rundunar yan sanda ta jihar Imo tayi nasarar kashe wasu yan ta'adda guda uku sa'annan ta ceto mutum bakwai da akayi garkuwa da su

-Mai magana da yawun hukumar na jihar ne ya bayyana hakan, inda ya kara da cewa komishinan yan sanda na jihar ya jagoranci aikin da kanshi

Rundunar yan sanda da ke aikin “Operation Puff Adde” a jihar Imo ta samu nasarar kashe wasu yan a’adda guda uku sa’annan kuma ta kwato wasu mutane guda bakwai da akayi garkuwa da su a dajin Lille dake kananan hukumomin Ohaji da Egbema.

Mai magana da yawun rundunar na jihar Imo, SP Orlando Ikeokwu, ya bayyana cewa komishinan yan sanda na jihar, Rabi’u Ladodo ne ya jagoranci samamen da aka kai.

Ya bayyana cewa komishinan yan sandan ya samu rakiyar kwamandojin da yawa ciki hada mataimakin komishina na ayyuka. Ya kuma bayyana cewa an tattaro wasu shaidu da yawa da aka samu a mafakar masu yin garkuwa da mutanen.

KARANTA WANNAN: Miyetti Allah ta karyata bidiyon da aka ga ana ma Fulani korar kare a Enugu

Ya bayyana cewa wannan aikin na daga cikin kudirin komishinan na ganin cewa rundunar yan sanda ta samu aminci daga wajen mutane akan cewa za su iya kare rayukansu da dukiyoyinsu a fadin jihar.

A yau Asabar 6 ga watan Yuli Legit.ng ta ruwaito cewa yan ta’addan Zamfara sun sako a kalla mutane 40 don cika daya daga cikin sharuddan yarjejeniyar sulhu da aka kulla tsakanin yan ta’addan da jami’an tsaro a jihar.

Hakan ya biyo bayan da yan kungiyar tsaro ta sa kai suka danka wasu Fulani 25 da suka kama tun cikin watan Afirilu ga komishinan yan sanda na jihar da niyyar a sake su idan yan ta’addan suka saki mutanen da suka kama.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel