Gwamnatin tarayya za ta dauki yan NYSC da yan Npower aiki don samar da tsaro

Gwamnatin tarayya za ta dauki yan NYSC da yan Npower aiki don samar da tsaro

-Gwamnatin tarayya da na jihohi na duba yiyuwar daukar yan sandan sa akai don magance matsalolin tsaro a kasar nan

-Shugaban kungiyar gwamnoni, Kayode Fayemi ne ya bayyana haka bayan da suka gama ganawa shugaba Buhari

-Ya bayyana cewa sun yanke wannan shawara bayan da suka ga cewa yan sanda 10,000 da za dauka ba za su isa ba wajen samar da tsaro a kasar nan

Gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi na aiki don ganin yadda za a karfafa rundunar yan sanda ta hanyar daukan yan bautar kasa da daliban da suka kammala jami’a da kuma ma’aikatan Npower don samar da tsaro.

Kayode Fayemi, shugaban kungiyar gwamnoni ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da yan jarida bayan sun gama ganawa da shugaba Buhari a ranar Juma’a 5 ga watan Yuli 2019.

Ya bayyana cewa sun duba sun ga cewa daukar yan sanda 10,000 ba zai isa ba a magance matsalolin tsaro da ake fuskanta.

A cikin watan Mayu, mukaddashin babban sifeton yan sanda, Muhammad Adamu ya bayyana cewa shugaba Buhari ya bashi umurni da ya gaggauta tabbatar da tsarin samar da tsaro a cikin garuwa a duk fadin Najeriya.

KARANTA WANNAN: Kotun zaben shugaban kasa: Atiku ya gabatar da hujjoji 26,000 don tabbatar rinto akayi masa

Adamu ya bayyana cewa “Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya umurce ni da in gaggauta tabbatar da sabon tsarin samar da tsaro a fadin kasar nan. A wannan sabon tsarin, shugabannin gargajiya za su samu cikakken iko na lura da dabi’u da al’adun mutanensu.”

“Wadannan kuratan na musamman za a dauke su ne daga kauyukansu don su yi aiki a matsayin yan sandan sa akai a karkashin kulawar rundunar yan sanda."

Ya bayyana cewa wannan sabon tsarin na samar da tsaro ta hanyar anfani da yan sandan sa kai shi ne irin tsarin da ake amfani da shi a kasar birtaniya kuma za a saisaita shi ta yadda zai yi daidai da tsarin tsaro na gargajiya da ake da shi a arewacin Najeriya.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel