KOGI: APC ta goyi bayan Yahaya Bello na yin zaben fidda gwani a asirce

KOGI: APC ta goyi bayan Yahaya Bello na yin zaben fidda gwani a asirce

-Kwamitin zartarwar APC na kasa ya aminta da kudurin Yahaya Bello inda ya ce zaben fidda gwani a Kogi a asirce za'a yi shi

-Sakataren yada labarin jam'iyyar Lanre Isa ne ya bada wannan sanarwar a ranar Juma'a jim kadan bayan da kwamitin ya kammala wata ganawa ta musamman a Abuja

Kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC na kasa ya aminta da yin zaben fidda gwamni a asirce domin fidda dan takara a zaben dake tafe na gwamnan jihar Kogi.

A wani zance da ya samu sanya hannun sakataren yada labaran jam’iyyar Malam Lanre Isa Onilu ya ce, an bayyana wannan jawabin ne bayan da kwamitin ya kammala wata ganawa a ranar Juma’a inda aka tattauna batun zaben fidda gwani na zaben gwamnan Kogi.

KU KARANTA:Zaben Zamfara: Kotun korafin zabe ta dage sauraron karar zaben Gwamna

Zancen kwamitin zartarwar jam’iyyar ya rinjayar da zaben cewa zai kasance ne a asirce inda ya yi watsi da maganar yin zaben ‘yar tinke kamar yadda wani bangaren jam’iyyar a jihar Kogin ya nema.

Bincike ya nuna cewa, ‘yan takarar gwamnan Kogi 21 dake karkashin jam’iyyar APC sun bayyana aniyarsu a fili ta son zaben fidda gwani ya kasance ‘yar tinke wanda ya sabawa abinda Gwamna Yahaya Bello ke so ayi.

Bangaren ya bayyana cewa, sake tsayar da Yahaya Bello zai iya kawo cikas ga jam’iyyar APC a jihar Kogi. Bugu da kari daga cikin ‘yan takarar akwai, Mustapha Mona Audu ( dan gidan marigayi tsohon gwamnan Kogi Prince Audu), Alhaji Aliyu Zakari Jiya, Dakta Aminu Musa Audu, Farfesa Saidu Muhammad Oga, Kashim Ali da wasu mutum 16.

Amma sai dai kwamitin zartarwar ya riga da yanke hukuncin cewa, “ Ba za ayi zaben yar tinke ba a wurin fidda gwani na gwamnan jihar Kogi, a asirce za'a gudanar da wannan zaben na fidda gwani.” A cewar Lanre Isa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel