Hajjin Bana: An bayyana irin illar da Boko Haram ta yi wa maniyyata a Borno

Hajjin Bana: An bayyana irin illar da Boko Haram ta yi wa maniyyata a Borno

Rikicin kungiyar Boko Haram da aka kwashe shekaru ana fama da shi ya jefa mafi yawancin mazauna Borno cikin talauci inda ya rage adadin mutanen da ke iya biyan kudin zuwa aikin hajji da kimanin kashi 70 cikin 100 a jihar.

Sakataren Hukumar Kula da Jin Dadin Maniyyata na Jihar, Dakta Mustapha Muhammad Ali ya shaidawa Kanem Trust cewa, "A baya muna samun masu zuwa aikin hajji fiye da 4,000 amma a yanzu wadanda muke da su ba su kai 1,500 ba."

"Rikicin ya janyo tabarbarewar kasuwanci. Mafi yawancin mutanen da ke kasuwanci su samu kudin zuwa aikin hajji suna sansanin 'yan gudun hijira suna fama da yadda za su kula da kansu."

DUBA WANNAN: Kannywood: Adam Zango ya nuna sabuwar babbar mota ta miliyan N23m da ya saya

Ya ce rashin tabbataccen tsaro a jihar ya ce janyo talauci kuma yana sanya mutane da dama yin hijira daga jihar.

Dr Ali ya ce jihar tana sa ran za ta samu maniyatta 1,500 duk da cewa Hukumar Aikin Hajji Ta Kasa (NAHCON) ta bawa jihar guraben mutane 2,056 a 2019.

Ya ce a makon da ta gabata, mutane 1,010 sun biya kudaden kujerunsu inda ya kara da cewa, "har yanzu muna karbar kudin kujera daga mutane. Muna fatan samun mutane 1,500 a wannan shekarar domin wadanda kananan hukumomi da gwamnatin jiha za ta biya wa hajji suna nan zuwa."

Sakataren Hukumar Aikin Hajjin ya ce N1, 444, 443.57 kudin kejurar hajji a Borno a wannan shekarar bayan an rage N51, 170.45 daga ainihin kudin kujerar da aka fara sanarwa da farko.

Ya yi kira ga maniyyatan jihar da ba su cika kudin kujerar su ba suyi gaggawan yin hakan kafin ranar Litinin 15 ga watan Yuli da za a rufe karbar kudin kujarar hajjin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel